Ku Dena Yi Mana Kamfen a Wurin Ibada, Shehin Malami Ya Ja Kunnen Ƴan Siyasa

Ku Dena Yi Mana Kamfen a Wurin Ibada, Shehin Malami Ya Ja Kunnen Ƴan Siyasa

  • Sheikh Habeebullaah El-Ilory ya yi gargadi kan yadda yan siyasa ke mayar da filin idi wurin yakin neman zabe a Kwara
  • Shaihin malamin ya yi wannan gargadin ne yayin addu'a ta musamman da aka shirya don marigayi Abdulganiyu AbdulaRazak
  • Sheikh El-Ilory ya gargadi mutane da su guji kawo siyasa wurin ibada domin hakan na iya janyo fushin Allah SWT

Ilorin, Jihar Kwara - Babban malamin addinin musulunci a Ilorin, Jihar Kwara, Sheikh Habeebullaah El-Ilory, ya soki yadda ake mayar da wurin ibada, filin idi, wurin yin kamfen din yan siyasa, rahoton The Guardian.

El-Elory, wanda ya bayyana cewa hakan babban saɓo ne, ya yi kira ga musulmi su dena yin hakan domin gudun fushin Allah SWT.

Ku Dena Yi Mana Kamfen a Wurin Ibada, Shehin Malami Ya Ja Kunnen Ƴan Siyasa
Sheikh Habeebullaah El-Ilory. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

The Guardian ta ruwaito cewa ya yi magana ne a jiya Lahadi yayin da manyan mutane daga sassan Nigeria suka hallarci addu'a da aka shirya don kwamishinan kudi na farko na jihar Kwara, Abdulganiyu AbdulaRazak, wanda ya rasu a bara.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

AbdulaRazak, wanda shine lauya na farko a arewacin Nigeria kuma minista a Jamhuriya ta farko ya rasu ne a ranar 25 ga watan Yulin 2020 yana da shekaru 93. Shine mahaifin gwamnan Kwara na yanzu AbdulRahman Abdulrazak.

Manyan mutanen da suka hallarci taron

Manyan yan Nigeria da dama sun hallarci addu'ar ta shekara daya da dansa, sabon Matawallen Ilorin, Dr Alimi AbdulRazak da yan uwansa suka shirya.

Gwamnan ya jagoranci mutane da dama zuwa taron. Mataimakin gwamnan jihar, Kayode Alabi; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Salihu Danladi; Kwamishinoni, masu sarautar gargajiya, shugabannin addini da malaman makarantu, yan siyasa da yan kasuwa duk sun hallarci taron.

Balogun na Gambari, Alhaji Muhammad Adebayo, ne ya wakilci Sarkin Ilorin, Dr Ibrahim Sulu-Gambari a wurin taron.

Babban limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir ne ya jagoranci addu'oin marigayin, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikansa sannan ya albarkaci iyalan da ya bari a baya.

Ya yi magana kan wasu abubuwa da suka shafi addini, zamantakewa da tattalin arziki da siyasa a jihar ciki har da rikicin siyasa da aka samu yayin Sallar Idi a Ilorin wanda ya yi Allah wadai da hakan yana mai cewa ya sabawa musulunci.

Kara karanta wannan

Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

Ya ce:

"Wurin sallar Idi ba wuri ne na siyasa da dabbanci ba. Ba za a amince da shi ba kuma ya kamata mutane su dena."

Ya bayyana marigayi AbdulRazak a matsayin abin alfaharin Nigeria ya kuma shawarci yaransa su yi koyi da halayensa na girmama ilimi, rashin girman kai, da kaunar yan adam da cigaba.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: