Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda

Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda

  • Hukumar ‘yan sandar jihar Kano ta musanta labarin kaiwa tawagar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero hari
  • Dama labarai sun yi ta yawo a ranar Lahadi akan harin da aka kaiwa tawagar sarkin farmaki a hanyar Zaria zuwa Kano
  • Saidai Kakakin ‘yansandan jihar ya musanta batun inda yace hatsari ne ya afkawa motar karshen tawagar sarkin ba hari ba

A ranar Lahadi ne hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta labaran da suka yi ta yawo akan harin da aka kaiwa tawagar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Labarai sun yi ta yawo akan yadda aka kaiwa tawagar sarkin hari akan hanyar Zaria zuwa Kano a ranar Lahadi, Kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Saidai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce hatsari ne ya auku da motar karshen tawagar sarkin ba wai hari aka kaiwa sarkin ba.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bankado yunkurin harin 'yan bindiga, sun ceci mutum 8 a Katsina

Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda
Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a

Kamar yadda Kiyawa yace, “Hatsari ne ya ritsa duk da su.

“Sarkin Kano yana tafe da tawagarsa daga Gadar Lado zuwa Dangi karkashin Pass. Suna hanya wata mota kirar Toyota Corolla ta ci karo da motar karshen a tawagar sarkin.

“An garzaya da direban Toyota Corollan zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad don a duba lafiyarsa.”

Daily Trust ta tattara bayanai akan yadda sarkin yake hanyarsa ta dawowa daga asibitin musulmi na Ahmadiyya akan titin Zaria dake Kano.

An yi iyakar kokarin ji daga fadar sarkin amma sam bai yuwu ba, duk da kokarin kiran sarkin gida, Alhaji Ahmad Ado Bayero, amma baya dauka.

Kuma bai mayar da martani ba na sakon da aka tura mishi a lokacin da ake rubuta rahoton nan.

A wani labari na daban, Sunday Adeyemo, mai rajin kwatar kasar Yarabawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa kutsa mishi gida inda yake bukatar a biya shi naira biliyan 5.5.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli. Sakamakon hakan an kashe mutane 2 kuma an kama mutane 12 lokacin.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Igboho ya ce yana cikin gidan shi a lokacin amma jami’an DSS basu gan shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: