Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

  • Dalibai uku na makarantar Bethel Baptist dake Kaduna sun sake tserowa daga hannun 'yan bindiga
  • An tattaro cewa daliban sun kwashe kwanaki biyar a daji suna yawo kafin su samu makiyayin da ya nuna musu hanya
  • Daya daga cikin daliban uku da ya haddace lambar wayar mahaifinsa ne ya kira shi inda yaje ya daukesu a Kasuwar Magani

Kaduna

Dalibai uku na babbar makarantar Bethel Baptist dake Kaduna sun tsero daga hannun miyagun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su.

Daily Trust ta tattaro cewa daliban sun tsero daga sansanin 'yan bindiga inda aka ajiyesu tun daga ranar 19 ga watan Yulin,2021.

Wani 'yar uwar daya daga cikin daliban mai suna Funmi, ta tabbatarwa da Daily Trust aukuwar lamarin a ranar Litinin.

KU KARANTA: Ku tsamo dukkan miyagun dake cikinku, Sarkin Muri ga shugabanni Fulani

Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane
Da duminsa: Karin daliban Kaduna 3 sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutane. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ba harar tawagar Sarkin Kano aka yi ba, hatsari ne ya ritsa da su, Rundunar 'yan sanda

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace sojojin Najeriya 2 akan wata babbar hanya a Borno

Dalibai sun yi kwanaki 5 suna yawo a daji

Kamar yadda tace, daliban uku sun kwashe kwanaki biyar suna yawo a cikin daji kafin daga bisani su hadu da wani makiyayi wanda ya nuna musu hanyar fita daga dajin.

An dauko su a Kasuwar Magani

An tattaro cewa daya daga cikin daliban da ya tsero ya iya tuna lambar wayar mahaifinsa kuma ya ari waya inda ya kira mahaifinsa wanda ya je ya dauko su.

"An ga yaran wurin Kasuwar Magani a yammacin ranar Lahadi bayan masu garkuwa da mutane sun sako dalibai ashirin da takwas. Hukumar makarantar cewa ta kira sirikina inda ya sanar damu," tace.

A baya, dalibai biyu sun tsero daga hannun masu garkuwa da mutanen kafin daga bisani 'yan sanda su samo su.

A wani labari na daban, bayyanar bidiyon wani bahaushe yana zubar da ruwan kudi a wani biki ya janyo surutai kala-kala daga masu kallo.

Kara karanta wannan

An gano yaran makarantar Islamiyyar Tegina a yankin Shiroro

Wannan bidiyon ya bayyana ne bayan kwanaki kadan da aka ga bidiyon wani dan kasuwa mai arzikin gaske dan kudancin Najeriya yana watsa kudi a bikin mutuwar mahaifiyarsa da aka yi a jihar Anambra.

Wasu har cewa suka yi bahaushen ya yi gasa ne da Cubana bayan ganin bidiyonsa yana ambaliya da kudi.

Mai wankin mota ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci Ganin bidiyon a kafafen sada zumunta ya janyo maganganu wanda wata @ijeomadaisy ta wallafa a shafinta na instagram.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel