Ruwan daloli: Bidiyon bahaushe yana watsi da daloli a liyafar biki ya janyo cece-kuce
- Bayyanar bidiyon wani bahaushe yana manna kudade masu yawan gaske a wani biki ya janyo cece-kuce
- Jama’a da dama sun yi ta surutai akan yadda yake watsa kudaden suna cewa kamar yana kwafar Obi Cubana ne
- Dama makwanni kadan da suka shude ne aka ga Cubana yana manna kudade masu yawa yayin birne mahaifiyarsa a Anambra
Bidiyon ruwan daloli - Bayyanar bidiyon wani bahaushe yana zubar da ruwan kudi a wani biki ya janyo surutai kala-kala daga masu kallo.
Wannan bidiyon ya bayyana ne bayan kwanaki kadan da aka ga bidiyon wani dan kasuwa mai arzikin gaske dan kudancin Najeriya yana watsa kudi a bikin mutuwar mahaifiyarsa da aka yi a jihar Anambra.
KU KARANTA: Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a
Bahaushe yayi gasa da Cubana
Wasu har cewa suka yi bahaushen ya yi gasa ne da Cubana bayan ganin bidiyonsa yana ambaliya da kudi.
Ganin bidiyon a kafafen sada zumunta ya janyo maganganu wanda wata @ijeomadaisy ta wallafa a shafinta na instagram.
A bidiyon an ga saurayin yana watsa kudade yayin da wata wakar hausa take tashi. Ma’auratan suna kwasar rawa yana watsa kudin.
Martanin jama'a kan bidiyon
Take anan wani mr_onyekacharles yace: “Yanzu babu mai magana, idan da dan kabilar ibo ne sai a fara tambayar inda ya samu kudin.”
Theluxurycommodity.ng yayi tsokaci da: “Abin babu burgewa dai, duk abin bahaushe dai daban yake.”
KU KARANTA: Buhari ga 'yan siyasa: Kada ku yi amfani da ni wurin yaudarar masu saka kuri'a
A wani labari na daban, mummunan alhini ya fada jihar Gombe yayin da wani Manjo Auwal Danbabu Mohammed, matarsa Fadila Auwalu Shehu Brema da diyarsa Aisha suka rasa rayukansu yayin wani mummunan hatsarin mota dasuka gwabza.
Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya ya samu labarin mai cike da alhini kuma ya kwatanta shi babban rashi ga jihar da jama'ar jihar.
Hatsarin ya faru ne a kan babban titin Zamfara zuwa Kano yayin da iyalan suke kan hanyar komawa sansaninsa bayan shagalin sallah, tribune online ta ruwaito.
Har zuwa lokacin rasuwarsa, Manjo Auwal Danbabu yana aiki ne da birged ta 1 ta rundunar sojin kasa dake Gusau a jihar Zamfara.
Asali: Legit.ng