Yan Bindiga Sun Sake Aikewa da Sako Ga Iyayen Daliban Bethel Baptist Kaduna
- Ɓarayin da suka sace ɗalibai a makarantar Bethel Baptist sun ce ba zasu saki dukan ɗaliban lokaci ɗaya ba
- Yan bindigan sun shaidawa shugabannin cocin Baptist cewa kashi-kashi zasu sako ɗaliban
- A kwanan nan ne ɓarayin suka sako kashin farko wanda ya ƙunshi ɗalibai 28
Shugaban yan Baptist reshen jihar Kaduna, Ishaya Jangado, yace za'a sako ragowar daliban makarantar Bethel Baptist kashi-kashi, kamar yadda the cable ta ruwaito.
Adadin ɗalibai 121 ne aƙa sace lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari makarantar ranar biyar ga watan Yuli.
Da farko ɓarayin sun sako ɗalibi ɗaya saboda matsalar da ta shafi lafiya yayin da jami'an yan sanda suka kuɓutar da wasu guda biyu.
Ɓarayin sun aje 28 daga cikin ɗaliban a wani wuri kan hanyar Kaduna-Abuja ranar Asabar da daddare, inda jami'an sa kai JTF suka ɗauke su zuwa sansanin soji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin cocin Baptist Kaduna bisa jagorancin shugaban Baptist na ƙasa, Israel Akanji, sune suka amso ɗaliban a hannun sojoji ranar Lahadi.
Za'a sako sauran ɗalibai 87
Bayan haɗa ɗaliban da iyayensu, da yawan waɗanda ba suga yayansu ba sun shiga damuwa sosai.
Jangado yace: "Mun yi magana da yan bindigan kuma sun shaida mun zasu saki ɗaliban ne kashi-kashi, ga shi yanzun sun sako kashin farko na 28."
"Ina kira ga sauran iyaye da basu ga yayansu ba a cikin waɗanda aka sako da kar su tafi domin za'a sako ragowar da yardar ubangiji. idan babu ɗanka a ciki nan kada ka cire tsammani, mu cigaba da addu'a."
A nasa ɓangaren, Israel Akanji, yace an yi duk wani kokari da ya kamata domin tabbatar da an sako ɗaliban, amma babban abinda aka fi maida hankali akai shine addu'a.
Yace: "Mun yi magana da jami'an tsaro, mun yi da gwamna kuma ya tabbatar mana zai yi iyakar bakin kokarinshi don a sako yaran."
"Gaba ɗaya yanzun ɗalibai 34 cikin 121 sun dawo, muna jiran dawowar ragowar ɗalibai 87."
Shin an biya kuɗin fansa?
Akanji ya ƙara jaddada cewa cocin su ba ta biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa domin a sako ɗaliban.
Yace: "Bansan a ina wasu suka samu bayanai ba, naji wasu labarai a kafafen watsa labarai, wasu na cewa mun biya miliyan N60m, wasu na cewa miliyan N100m muka biya."
"Abinda muka sani a cocin mu shine, ba zamu biya kuɗin fansa ba saboda ba dai-dai bane ka biya kuɗi ga mutanen da suka aikata laifi ba."
A wani labarin kuma Dattijon da Yaje Kai Kudin Fansa Miliyan N30m Ya Kubuta, Ya Fadi Halin da Daliban Islamiyyar Tegina Ke Ciki
Mutumin da yan bindiga suka riƙe daga kai kuɗin fansa miliyan N30m ya dawo. Kasimu Barangana ya bayyana cewa ɓarayin sun ba shi kulawa yadda ya kamata lokacin zamansa a wurinsu.
Dattijon ya bayyana cewa ɗaliban suna cikin mummunan hali a hannun yan bindigan da suka sace su.
Asali: Legit.ng