Rahoton tsaro: Yadda 'yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojojin Kamaru

Rahoton tsaro: Yadda 'yan Boko Haram suka kai hari sansanin sojojin Kamaru

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka wasu sojojin kasar Kamaru da dama ranar Asabar
  • Rahoto ya bayyana cewa, 'yan ta'addan sun kai hari ne kan wani sansanin na sojoji a Kamaru
  • Sai dai, an hallaka wasu daga cikin 'yan ta'addan da ba a tantance adadinsu ba har zuwa yanzu

Mayakan Boko Haram sun mamaye wani sansanin sojoji a yankin Arewa mai nisa na Kamaru a ranar Asabar 24 ga watan Yuli, 2021, inda suka kashe a kalla sojoji bakwai tare da jikkata wasu da dama, in ji majiyar sojoji wasu da daban.

Sun buge sansanin da ke yankin Sagme da misalin karfe 4.00 na safiyar ranar Asabar, kamar yadda sojoji biyu da wani mazaunin yankin suka shaida wa Xinhua.

Maharan, wadanda ke dauke da muggan makamai, wasu daga cikinsu cikin shigar sojoji sun zo ne cikin jerin gwanon motoci shida, in ji wani soja.

Rahoton tsaro: Yadda 'yan Boko Haram suka hallaka sojojin kasar Kamaru da dama
Sojojin Kamaru: guardian.ng
Asali: UGC

Bayan an kwashe sa’o’i ana fada, an kashe kwamandan sansanin sojoji tare da abokan aikinsa shida.

Kara karanta wannan

Kisar Ƴan Sanda: Mutane Sun Tarwatse Yayin da Sojoji Suka Dira Wani Gari a Enugu

Wani soja da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa:

“Sojojin sun nuna jarumtaka kuma sun kare kansu da karfi."
“Abun godiya ne saboda sun sami nasarar fatattakar maharan kuma sun ceci rayuka da yawa."

Sojan ya kara da cewa har yanzu ba a san adadin rayukan da sojoji suka mika lahira daga bangaren 'yan ta'addan ba.

'Yan Boko Haram sun addabi sojojin Kamaru

Harin na ranar Asabar shi ne mafi muni a kan sojojin Kamaru a cikin sama da watanni 10, a cewar rahotannin tsaro.

Kungiyar Boko Haram ta addabi yankin Arewa mai nisa na Kamaru tun daga shekarar 2014, inda suka kashe mutane sama da 2,000, a cewar rahotannin tsaro, The Guardian ta ruwaito.

'Yan Boko Haram da ISWAP 28 sun mika kansu ga rundunar sojin Najeriya

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da na ISWAP 28 da iyalansu da suka tsere sun mika kansu ga dakarun rundunar bataliya ta 151 a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Sojoji Sun Fatattaki Mayaƙan Boko Haram Daga Wani Gari a Yobe

Mai magana da yawun rundunar sojin Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, BBC ta ruwaito.

Sanarwar ta ce mayakan da suke tsere wa hare-haren sama da ake kai musu sun mika wuya ne ga dakarun bayan da aka fi karfinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel