Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa

Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa

  • Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa yin kutse a gidansa inda yake bukatar naira biliyan 5.5
  • Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli inda har aka kashe mutane 2 kuma aka kama mutane 12
  • Dama an kama Igboho da matarsa ne a babban filin jirgi sama dake Cotonou a ranar Litinin sannan aka gabatar dashi a gaban alkali

Sunday Adeyemo, mai rajin kwatar kasar Yarabawa wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya maka gwamnatin tarayya a kotu bisa kutsa mishi gida inda yake bukatar a biya shi naira biliyan 5.5.

Jami’an hukumar DSS sun kutsa gidan Igboho dake Ibadan a ranar 1 ga watan Yuli. Sakamakon hakan an kashe mutane 2 kuma an kama mutane 12 lokacin.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Igboho ya ce yana cikin gidan shi a lokacin amma jami’an DSS basu gan shi ba.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke 'yan sa kai 7, sun bankawa motar yaki wuta

Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa
Igboho ya maka FG a kotu, yana bukatar N5.5bn na diyyar kutse a gidansa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Kotu a Kano ta haramtawa majalisar jiha binciken Rimingado

Saidai an kama shi a babban tashar jirgin sama dake Cotonou a jamhuriyar Benin a ranar Litinin. An gabatar dashi a gaban alkali a Cour De’appal De Cotonou.

Lauyansa , Yomi Aliyu, ya gabatar da bukatar masu rajin kare hakkin bil’adama a babbar kotun dake Ibadan inda yake bukatar ga gwamnatin tarayya.

Ya hada har da Antoni janar da hukumar DSS a korafin nasa, ChannelsTV ta ruwaito.

Kamar yadda ya gabatar da korafin: “Sakamakon kutse da lalata masa dukiya a gidansa da misalin 1am zuwa 3am wanda hakan ya yi karantsaye akan hakkin bil’adama kuma wajibi ne gidansa ya samu kariya bisa kundin tsarin mulkin Najeriya, bangare na 37, 43 da 44 na 1999 .

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta umarci DSS da su gabatar da mukarraban Igboho 12 da suka tsare

“Sannan hukumar ta dakatar da Igboho daga nema wa Yarabawa hakkinsu inda tayi ta kai masa farmaki da bindiga don nemansa a raye ko a mace duk da cewa mutum ne shi mai neman zaman lafiya.

“Sakamakon haka yana rokon kotu mai alfarma da ta umarci gwamnatin tarayya ta biya shi naira biliyan 5 akan shiga hakkinsa."

Sannan takarda ta bukaci wadanda ake kara da su bayar da hakuri sakamakon cutar da Igboho da suka yi.

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa ta yi ikirarin cewa ba a rasa rai ko daya ba kuma babu bam ko daya da ya tashi yayin bikin babbar sallah balle a kai ga harin 'yan bindiga ko na 'yan ta'adda.

Femi Adesina, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook mai taken "Ubangiji ya albarkaci dakarunmu."

Kara karanta wannan

Matashi daga jihar Kano zai tsaya takarar shugaban kasa a APC, ya gana da manya kan batun

Kamar yadda takardar tace, Adesina ya nuna tabbacinsa na cewa kalubalen tsaron da ke addabar kasar nan baki daya ya kusa zama tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel