Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP Na Kasa Tare da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP Na Kasa Tare da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheka Zuwa APC

  • Guguwar sauya sheƙa ta tafi da tsohon shugaban matasan PDP da wasu jiga-jigai zuwa APC a Ondo
  • Gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, shine ya karbi sabbin mambobin APC a Sakateriya dake Akure
  • Yace jam'iyyar APC zata rike su ba tare da nuna banbanci ba, babu tsoho babu sabo a cikin jam'iyyar

Tsohon shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa, Dennis Niyi Alonge, ya jagoranci tawagar wasu jiga-jigan jam'iyyar zuwa APC a ƙarshen makon nan a jihar Ondo, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Shugaban rikon kwarya na jihar, Engr. Ade Adetimehin, shine ya tarbe su, inda ya miƙa su ga jagoran APC na jihar kuma Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, a sakateriyar jam'iyyar dake Akure.

Alonge-Niyi, wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ose ne ya sauya sheƙa zuwa APC tare da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Akoko ta Kudu-Gabas, Hon Akin Aibinuomo, tsohon shugaban PDP na yankin Irele, Prince Thompson Atayase da ɗarururwan magoya bayansu.

Kara karanta wannan

Ba da Jimawa Ba Wasu Jiga-Jigan Gurbatattun Yan Siyasa Zasu Sauya Sheka Zuwa APC, Shugaban ADC

Jiga-Jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a Ondo
Shugaban Matasan Jam'iyyar PDP Na Kasa Tare da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheka Zuwa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Babu nuna banbanci

Da yake karɓan sabbin yan APC, Gwamna Akeredolu, ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna banbanci ba tsakanin mambobin jam'iyyar.

Ya ƙara da cewa a shirye APC take ta karbi duk wanda yake son shigowa cikinta, kuma ba tare da nuna banbanci ba.

Gwamnan yace: "Inason jawo hankalin shugabannin jam'iyyarmu, bai kamata a nuna musu banbanci ba tunda sun zama mambobin APC."

"Ya kamata mu nemo wasu hanyoyin da zamu sanya su a cikinmu, domin canza su zuwa yan APC zalla, ba tsoho ba sabo."

Babu kamar APC

Shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar Ondo, Adetimehin, yace APC ta yi zarra a jihar.

Yace: "Gwamna Akeredolu ya canza sa'ar APC zuwa mai kyau, ya canza jihar zuwa mai dogaro da kanta. Amma kafin zuwan shi an dogara ne da ayyukan gwamnati."

Da yake jawabi a madadin sauran, Alonge-Niyi, yace:

"Nasarorin da gwamnatinka ta samu tun zuwanta sune na farko da duka jawo hankalinmu muka dawo APC."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Asali: Legit.ng

Online view pixel