Ba aikin mu bane dakatar da masu fafutuka , sai dai ba za mu laminci rikici ba - Rundunar Sojoji
- Sojojin Najeriya suna da kundin tsarin mulki da bai basu damar dakatar da masu fafutuka daga gudanar da zanga-zanga ba
- CDS General Lucky Irabor ne ya bayyana wannan a yayin wata tattaunawa da tsaffin masu yi wa kasa hidima a Imo a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli
- Amma duk da haka, Irabor ya ce sojoji ba za su taba yarda da tashin hankali daga duk wanda ayyukansa ke dagula zaman lafiya a kasar ba
Babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS) Janar Lucky Irabor ya ce ba aikin sojoji ba ne su dakatar da masu fafutukar siyasa da masu neman ballewa daga shirya kamfen dinsu a Najeriya.
Janar Irabor yayi wannan bayani ne a Imo a ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, yayin tattaunawarsa da hafsoshin kudu maso gabas da suka yi ritaya, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ba za mu lamunci rikici ba
Sai dai kuma, CDS din ya bayyana cewa koda sojoji suna da kundin tsarin mulki da zai hana su yiwa masu fafutukarsu katsalandan a yin taronsu, ba za ta lamunci tashin hankali daga kowa ba a kowani hali, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ya yi bayanin cewa:
"Ba aikin sojoji ba ne su dakatar da duk wani mai son yin fafutuka. Abu ne na siyasa, amma ba mu yarda da duk wani abu da zai jawo rikici ba kan irin wannan fafutukar.
“Muna da kundin tsarin mulki wanda ya tabbatar mana da hanyoyin da za mu bi domin shawo kan duk wani korafi. Me yasa sai kayi kisan kai kafin ka cimma burin ka?
“Don haka, duk wanda ya saba tanadin kundin tsarin mulki, ba shakka, mu a matsayinmu na hafsoshin soja ko jami’an tsaro ba za mu yarda da hakan ba.”
A wani labari na daban, hare-hare da dama da ‘yan bindiga suka kai a kan al’ummomin Benuwai da Nasarawa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 da asarar dukiyoyi.
A ranar Talata, an tattaro cewa kimanin mutane 13 aka kashe lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari kan wasu garuruwa a yankin Guma da ke Benue.
An kuma rahoto cewa maharan sun kuma auka wa garin na Torkula.
Asali: Legit.ng