Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara

Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara

  • Ganduje ya kai ziyarar gaisuwar Sallah gidan shugaban Kadiriyya
  • Gwamnan Kano ya tofa albarkacin bakinsa kan lamarin AbdulJabbar
  • Ganduje ya ce wannan aikin fafutukar tamu ce duka

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a karon farko ya yi furuci kan lamarin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara wanda Malaman Kano suka kai kara wajensa.

Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta bibiyi lamarin har zuwa karshe.

Ganduje ya bayyana hakan ne a jawabin da lokacin da ya kai ziyarar Barka da Sallah gidan Qadiriyya, Kabara domin yiwa Shugaban Darikar Qadiriyya na Africa Sheikh Qaribullahi Sheikh Nasiru Kabara gaisuwa.

Sheikh Qariballah Kabara babban yaya ne ga Malam AbdulJabbar.

Legit ta bibiyi wannan ziyara ta shafin hadimin Ganduje na kafofin yada labaran zamani, Abubakar Aminu Ibrahim wanda ya halarci ziyarar.

Gwamnan ya yabawa malaman jihar da sukayi muqabala da Abduljabbar game da tuhume-tuhumen da ake masa da batanci ga manzon Allah Annabi Muhammad (SAW).

Kara karanta wannan

Gaisuwar Sallah: Wasu ‘Yan Majalisar Tarayya da Gwamnoni 11 sun ziyarci Garin Daura

Gwamna Ganduje yace:

"Babu shakka wannan muqabala da aka shirya, Malamai sun yi aikin nasu na Malanta, kuma sun nuna cewa Masana ne
"Muna matukar farin ciki ganin cewa muna bin matakan da suka dace game da wannan batu. Kuma idan Allah ya yarda, gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da bibiya an ga karshn wannan al'amari."

Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara
Karo na farko, Ganduje ya yi magana kan lamarin AbdulJabbar Kabara Hoto: Abubakar Aminu Ibrahim
Asali: Facebook

Gwamna yasamu rakiyar Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, Sakataren Gwamnati Alh. Usman Alhaji, Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnati Alh. Ali Haruna Makoda.

Sauran sune Shugaban Jamiyyar APC na Jihar Kano Alh. Abdullahi Abbas, Kwamishinoni da Masu Bawa Gwamna Shawara, Kwamandan Hisba Sheikh Haruna Ibn Sina da Dattijan Jamiyyar APC na Jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel