An kama Chioma ta yi basaja da Hijabi dauke da miyagun kwayoyi masu nauyin kilo 465
- An kame mata biyu da suka yi badda bami da hijabi wajen safarar kwayoyi zuwa Arewa
- Sun ce dole ne sai sun sanya hijabi kafin a dauke su hoto tare da miyagun kwayoyin nasu
- Sun fito ne daga garin Onitsha a Jihar Anambra
Jami'an hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Benuwai sun kama wata mata 'yar shekara 36, Chioma Afam, tare da abokiyar aikinta, Peace Caleb, mai shekara 22.
Afam, wacce take amfani da sunaye da dama kuma take sanye da hijabi domin guje wa binciken tsaro, an ce an kama ta tare da abokiyar cin mushen nata ne yayin da suke kokarin safarar kwayoyin Diazepam da Exol-5 guda 296,000 daga Onitsha a jihar Anambra, zuwa jihar Gombe.
Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.
Ya ce,
“Chioma (Afam), wacce ke amfani da sunaye da daban daban kamar su Amina da Uzoamaka da Ifunaya domin badda bami, an kame ta ne a ranar Asabar, 17 ga Yuli, 2021, tare da wata mai suna Peace Chidinma Caleb mai shekara 22, wanda ita ma take sanye da hijabi a matsayin badda sawun munanan ayyukanta a lokacin gudanar da binciken yau da kullum na motocin da ke shiga Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.
“Motarsu da ta fito daga Onitsha, jihar Anambra, an tare ta a kan hanyar Makurdi-Alliade yayin da ta nufi jihar Gombe ta Makurdi.
“Binciken da aka yi wa motarsu ya kai ga gano kilogram 43 na kwayar Diazepam da kilo 33 na Exol-5, jimillar nauyinsu ya kai kilo 76 tare da wasu kwayoyi masu nauyin kilo 296,000 cike a cikin manyan jakunkunan Ghana-must-go.
Ya kara da cewa abin mamakin shi ne, masu fataucin miyagun kwayoyin biyu sun ki amincewa da kokarin daukar su hoto tare da kwayoyin ba tare da sun sanya hijabinsu ba.”
Hukumar NDLEA tayi ram da dan Achaba
A wani labarin makamancin wannan, rundunar NDLEA a Jihar Ondo a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli 2021, ta kame wani dan achaba, mai suna Olu Ameh, tare da kilo 465 na tabar wiwi a kan hanyar Ijagba-Ute a Karamar Hukumar Ose ta jihar.
A cewar hukumar NDLEA, an sayo haramtaccen maganin ne daga wani mai suna Joseph a Ago-Akure, a Karamar Hukumar Akure ta Arewa kuma ana kai wa mai sayan, Egbonwon da ke a kauyen Ijagba cikin Karamar Hukumar Ose.”
Asali: Legit.ng