Hayaƙin Janareto Ya Kashe Mutum Huɗu Ciki Har Mata Da Mijinta Yayin Bikin Sallah a Kwara

Hayaƙin Janareto Ya Kashe Mutum Huɗu Ciki Har Mata Da Mijinta Yayin Bikin Sallah a Kwara

  • Wasu mutane hudu sun riga mu gidan gaskiya a Kwara sakamakon shakar hayakin janareta
  • Wadanda suka rasun sun hada da maigida, matarsa, kawar matarsa da abokin dansa
  • Rundunar yan sanda ta jihar Kwara ta tabbatar da afkuwar lamarin ta gargadi jama'a su rika kula

Wani abin bakin ciki ya faru a jihar Kwara, a ranar Laraba, a yayin da hayaki daga janareta ya yi sanadin rasuwar mutane hudu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a gidan Ojomu a Snmora, karamar hukumar Irepdun a jihar ta Kwara.

Wadanda abin ya faru da su sun taho daga Legas ne domin yin bikin sallah a Kwara.

Hayaƙin Janareta Ya Kashe Mutum Hudu Yayin Bikin Sallah a Kwara
Hayaƙin Janareto Ya Kashe Mutum Hudu Yayin Bikin Sallah a Kwara. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

Daily Trust ta ruwaito cewa an kai gawarwakinsu wurin ajiyar gawa a babban asibitin Offa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari Kaduna, sun sace wasu mata da shanu masu yawa

Wasu mutane biyu da suka shaki hayakin janareton suna nan a asibiti ana basu kulawa bayan an gano su a sume.

Wata majiya ta ce DPO na Agbamu, Igbasan Owoyemi John, yana daga cikin wadanda suka zo kwashe gawarwakin.

A cewar majiyar:

"Mun gano gawaraki a safiyar yau, mai gida, matarshi da kawarta da abokin daya daga cikin yaran mai gidan da ya biyo su Legas domin bikin sallah.
"Wata dattijuwa da ke gidan ne ta gano gawarwakin a lokacin da ta tafi gaishe su da safe bayan karfe 7 a ranar Laraba.
"Biyu daga cikinsu da ke da rai an same su ne a sume da safen ranar Laraba. Sune kwance a asibiti rai hannun Allah kuma bamu san rannan da za a sallamo su ba."

Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar lamarin

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan uwa 3 sun sheka barzahu bayan sun kwashi garar Amala a Ilorin

KU KARANTA KUMA: Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa

Ya kara da cewa:

"Eh, yanzu na kira jami'an mu da ke wurin. Da gaske ne abin. Za mu cigaba da kira ga mutane su rika kula da lafiyarsu a lokutan bukukuwa. Muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan wadanda abin ya shafa."

Sarki Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya Ya Rasu a Kaduna

A wani labarin kun ji cewa Allah ya yi wa Dr Danjuma Barde, sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya a ƙaramar hukumar Chikun ya rasu.

Leadership ta ruwaito cewa basaraken ya rasu ne a safiyar ranar Laraba. Rahotanni sun ce ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna bayan jinya.

Peter Aboki, shugaban kungiyar cigaban Gbagyi, GDA, ya tabbatar da rasuwar basaraken.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro yana tarnaki ga ci gaban Najeriya - Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel