Hoton Sanatan Nigeria Ya Yi Durƙuso Kan Gwiwansa Gaban Tsohon Gwamna Da Ya Saci Kuɗin Jiha Ya Janyo Cece-Kuce

Hoton Sanatan Nigeria Ya Yi Durƙuso Kan Gwiwansa Gaban Tsohon Gwamna Da Ya Saci Kuɗin Jiha Ya Janyo Cece-Kuce

  • Wani hoton Sanata James Manager daga jihar Delta da tsohon mai gidansa James Ibori ya janyo cece-kuce
  • A cikin hoton, an gano sanatan ya yi durkuso kan gwiwansa a gaban tsohon gwamnan jihar da aka taba yi wa dauri a gidan yari kan sace kudin jiha
  • Mutane da dama a dandalin sada zumunta sunyi tir da hakan suna zargin sanata na neman yin takarar gwamna ne a 2023 shi yasa ya ke kamun kafa

Wani hoto da ke nuna sanata mai wakiltar Delta ta Kudu, James Manager, ya rusuna gaban tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ya bazu a dandalin sada zumunta, ya kuma janyo cece-kuce, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin hoton, an gano Manager sanye da atamfa da takunkumin fuska a kasar kuncinsa da kuma hannunsa a nade yayin da Ibori shi kuma yana zaune kan kujera mai launin baki da ja sanya da kaya mai ruwan bula.

Kara karanta wannan

Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure

Hoton Sanatan Nigeria Ya Yi Durƙuso Kan Gwiwowinsa Gaban Tsohon Gwamna Ya Janyo Cece-Kuce
Sanata James Manager Ya Yi Durkuso Gaban Tsohon Gwamna James Ibori. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Ibori ya rike mukamin gwamnan jihar Delta mai albarkatun man fetur daga 1999 zuwa 2007 amma daga bisani kotu ta same shi da laifin bannatar da biliyoyin naira na jiharsa yayin da shi kuma Manager sanata ne tun shekarar 2003.

Sai dai duk da daurin gidan yari da aka yi wa Ibori, har yanzu yana daga cikin masu fada a ji a jihar.

Menene dalilin da yasa Sanata James ya yi durkuso gaban James Ibori?

Wani na kusa da Sanatan ya tabatarwa The Punch ingancin hoton yana mai cewa rusunawa alama ce da girmama manya a kabilar Urhobo.

Ya ce:

"Sanatan ya kai masa ziyara a ranar Laraba. Ibori dattijo ne, sarki ne kuma yana gaba da shi, tunda tsohon mai gidansa ne. Duk lokacin da ka ziyarci wani babba ko wanda kake darajawa a kasar Urhobo, zaka rusuna. Alama ce ta girmamawa kuma na nuna wa mutane girmansa a wurinka. Ana jirkita abubuwa ne a dandalin sada zumunta. Alaka ce ta kusa. Ba za ka yi tsammanin sanatan ya masa magana a tsaye ba.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Minista ta ce maza su hakura kawai, a mika wa mata ragamar Najeriya

"Sanatan ya kai masa ziyara ne saboda ya dade bai ga Ibori don haka ya kai masa ababen sha. Ababen shan ne ke kan teburi a hoton."

Ra'ayin wasu mutane game da hoton James Ibori da Sanata James

Sai dai mutane da dama a dandalin sada zumunta na ganin abin da sanatan ya yi bai dace ba

Precious Erutase ta rubuta a Facebook:

"Eh, bana zagin mutane a dandalin sada zumunta amma wannan hoton abin alfahari bane da Sanata James Manager da hadiminsa. A gani na, hadiminsa ya dauki wannan hoton ne don ya nuna wa yan Delta azarbabin da mai gidansa ke yi na neman mulki.
"Duk Niger Delta, babu inda za ka samu mutum mai girma irin Sanata James Manager ya rusuna da kafansa a gaban wani mutumin da ba mahaifinsa ba, mutumin da watakila sa'ansa ne. A'a, wannan zubar da girma ne."

Ezekiel Ibok wanda ya ce shi malamin makaranta ne shima ya yi rubutu a Facebook:

Kara karanta wannan

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

"Sanata mai ci, James Ebiowu Manager mai wakiltar Delta ta Kudu ya rusuna a gaban James Ibori, yana neman goyon baya don takarar gwamna a 2023. Rusuna wa tsohon mai laifi da ya sace kudin jihar Delta?.
"Me yasa muke karrama barayi da masu almubazzaranci a Nigeria? Ta yaya muka tsinci kan mu a wannan halin? Ya tambaya."

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Kara karanta wannan

Idan ka biyewa Yariman Bakura zai kai ka ruwa, AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: