Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara

  • Miyagun 'yan bindiga sun harbo jirgin yakin NAF amma matukin jirgin yayi nasarar sauka da kumbo a wani kauye kusa da Dansadau
  • Mazauna kauyen sun gan shi inda suka yi hanzarin boye shi kafin duhu yayi suka bashi kaya ya canza sannan aka kaishi gidan hakimi
  • Washegari da safe jirage biyu na NAF tare da daya na yaki sun hanzarta zuwa garin Dansadau inda suka dauka matukin jirgin

Wasu mazauna yankuna a jihar Zamfara a ranar Litinin sun bada labarin yadda suka ceci matukin jirgin yaki jim kadan bayan ya sauka daga kumbo bayan hatsarin jirgin yakin a ranar Lahadi.

Har yanzu dai ba a san halin da sauran wadanda ke cikin jirgin suke ba, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi masu karfi sun sanar da Daily Trust cewa jirgin yakin ya fadi ne a wani yanki dake da kusancin kilomita 15 daga garin Dansadau.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Matukin jirgin NAF ya sha da kyar yayin da 'yan bindiga suka harbo jirgi

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara
Jirgin NAF: Yadda jama'a suka taimaki matukin jirgin da 'yan bindiga suka harbo a Zamfara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna Bello Matawalle: Arewa ita ce matsalar kanta da kanta

Wani mazaunin yankin ya ce: "Matukin jirgin saman ya sauka daga kumbo inda da gaggawa ya shiga yankin kusa. Bayan mutane sun gane abinda ya faru, sai suka yanke hukuncin boye shi ta yadda koda 'yan bindigan sun biyo shi ba zasu gan shi ba.

"An ga 'yan bindigan suna ta kaiwa da kawowa a inda jirgin saman ya fadi, ta yuwu neman wanda ya tsira suke yi."

Mazaunin yankin wadanda suka bukaci a boye sunansu sun ce: "Mauzauna yankin sun jira har faduwar rana sannan suka baiwa matukin jrigin kaya irin na kauyawa inda yayi basaja sannan suka fitar dashi zuwa garin Dansadau inda aka mika shi wurin hakimi."

"Da safe sai jiragen NAF biyu tare da na yaki daya suka iso domin ceton matukin jirgin. Jirgin ya sauka kusa da wata makarantar sakandare dake garin yayin da jirgin yakin ke ta kaiwa da kawowa. An mika musu matukin jirgin saman inda suka tafi da shi a take," wani ya sanar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin 'yan sanda a Zamfara sun kashe 13

A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta musanta rahotannin dake yawo na hatsarin da jrigin samanta ya kara yi a Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata.

Akwai rahotannin dake yawo na cewa jirgin sojojin saman Najeriya wanda ya taso daga jihar Adamawa ya fadi a wani wuri a cikin jihar Kaduna.

Amma kuma yayin da aka tuntubi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya sanar da TheCable cewa babu wani hatsari da ya auku a Kaduna kamar yadda ya sanar da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel