Ba Mu Hana Ƴan Nigeria Amfani Da Twitter Ba, Gwamnatin Tarayya Ta Faɗa Wa Kotu

Ba Mu Hana Ƴan Nigeria Amfani Da Twitter Ba, Gwamnatin Tarayya Ta Faɗa Wa Kotu

  • Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce bata hana yan kasa amfani da Manhajar Twitter ba
  • Gwamnatin ta ce duk da dakatarwar, yan Nigeria na cigaba da shiga Twitter da VPN
  • Gwamnatin ta ce za ta janye dakatarwar da ta yi wa Twitter da zarar ta yi rajista da NBC da CAC

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta fada wa babban kotun tarayya a Legas cewa bata hana yan Nigeria amfani da dandalin sada zumunta na Twitter ba, tana mai cewa har yanzu yan Nigeria da dama suna amfani da shi a kullum, rahoton The Punch.

Attoni Janar na kasa, Abubakar Malami, da gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne yayin bada amsa kan wani kara da lauya mai rajjin kare hakkin bil adama, Inihebe Effiong ya shigar game da batun na hana amfani da Twitter.

Ba Mu Hana Ƴan Nigeria Amfani Da Twitter Ba, Gwamnatin Tarayya Ta Faɗa Wa Kotu
Attoni Janar kuma Ministan Shari'a na Nigeria, Abubakar Malami (SAN). Hoto: The Punch
Asali: Facebook

A ranar 4 ga watan Yunin shekarar 2021 ne gwamnatin Nigeria ta dakatar da ayyukan Twitter kimanin kwanaki biyu bayan Twitter ta goge wani rubutu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a dandalin.

Kara karanta wannan

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

Sai dai, yan Nigeria da dama na amfani da manhajar VPN mai badda-kama domin amfani da manhajar na Twitter duk da dakatarwar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Malami, ciki wata sanarwa da ya fitar ya yi barazanar tuhumar yan Nigeria da ke cigaba da amfani da manhajar yayin da NBC ta umurci dukkan gidajen rediyo da talabijin su dena daukan labarai daga Twitter.

Lauyan mai rajjin kare hakkin bil adama, Effiong, ya yi karar Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, Malami, da gwamnatin tarayya bisa dakatar da Twitter.

A cikin karar Effiong ya nemi kotu ta hana gwamnati dakatar da amfani da manhajar ko hana mutane amfani da wasu dandalin sada zumuntar da wasu bukatu takwas da ya ce keta hakkin bil adama ne.

Dakatar da Twitter ta take hakkin bil adama bane

Sai dai, Mr Ilop Lawrece a madadin gwamnatin tarayya da AGF ya ce dakatar da Twitter ba take hakkin bil adama bane domin har yanzu yan Nigeria na cigaba da amfani da Twitter.

Kara karanta wannan

Yadda 'Yan Sandan 'Interpol' Suka Damke Sunday Igboho da Matarsa 'Yar Jamus

Ya kuma ce yan Nigeria na da damar bayyana ra'ayoyinsu da sukar gwamnati idan bukatar hakan ya tashi a wasu kafafen kamar WhatsApp, Facebook, Tiktok da wasu sauran.

Gwamnatin tarayyar ta kuma ce yan Nigeria su dena fushi da ita domin ba laifinta bane domin Twitter ta ki bin dokokin kasa.

Gwamnatin ta fadawa kotu cewa za ta janye dakatarwa da ta yi wa Twitter da zarar kamfanin ta yi rajista da NBC da CAC.

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

A wani labarin daban, kun ji cewa manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

Kara karanta wannan

Dole ne Gwamnatin Najeriya tayi bayanin yadda ta kama Nnamdi Kanu a Kenya - Birtaniya

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel