Dole ne Gwamnatin Najeriya tayi bayanin yadda ta kama Nnamdi Kanu a Kenya - Majalisar Dokokin Birtaniya

Dole ne Gwamnatin Najeriya tayi bayanin yadda ta kama Nnamdi Kanu a Kenya - Majalisar Dokokin Birtaniya

  • Birtaniyar ta hannun ofishin jakadancinta a Abuja ta nemi izinin gana wa da Nnamdi Kanu
  • Karamin Ministan Ingila, Lord Tariq Ahmad, ya bukaci gwamnatin Najeriya da tayi bayani yadda aka kama shi
  • Sannan Birtaniyar ta tabbatar cewa ita fa ba a cikin kasarta aka kame Nnamdi Kanu ba

Majalisar Dokokin Birtaniya ta bayyana cewa dole ne gwamnatin Najeriya ta yi bayanin irin rawar da ta taka da kuma yadda aka kame jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, daga kasar Kenya.

Karamin Ministan Birtaniyar, Lord Tariq Ahmad, ya nemi gwamnatin Najeriyar da ta bayyana wa gwamnatin Birtaniyar yadda ta dawo da jagoran na IPOBn.

Hakan ya biyo bayan wata muhawara ce da Majalisar Birtaniyar ta gudanar a ranar 7 ga watan Yuli, yayin da ’yan majalisar suka tattauna kan yadda gwamnatin Birtaniya ta tantance rawar da Kenya ta taka a kamen na Kanu.

Lord Alton na Liverpool ya tayar da batun a gaban zauren, yana neman magance ce-ce-ku-cen da ke tattare da batun dauko Kanu daga Kenya zuwa Najeriya ba da son ransa ba.

Kara karanta wannan

Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari

Ya kuma nemi sanin ko akwai wani taimako da ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja ya bayar ga shugaban kungiyar ta IPOB da ke cikin damuwa.

Dole ne Gwamnatin Najeriya tayi bayanin yadda ta kama Nnamdi Kanu a Kenya - Majalisar Dokokin Birtaniya
Dole ne Gwamnatin Najeriya tayi bayanin yadda ta kama Nnamdi Kanu a Kenya - Majalisar Dokokin Birtaniya
Asali: Original

Dangane da muhawarar majalisar, Ahmad ya ce,

"Muna neman bayani daga Gwamnatin Najeriya game da yanayin yadda aka kama tare da tsare Nnamdi Kanu."

Ahmad ya kuma tabbatar da ikirarin da Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Abuja ya yi na cewa gwamnatin Birtaniya na bayar da taimako ga Shugaban na IPOB.

"Ofishin jakadancin Birtaniya ya nemi izinin shiga inda aka tsare Kanu daga gwamnatin Najeriya, kuma a shirye muke mu ba da taimakon ga jagoran," inji shi.

Yayin da gwamnatin Buhari ta ki bayyana yadda ta dawo da jagoran haramtaciyyar kungiyar ta IPOB daga Kenya, gwamnatin Birtaniya ta yi karin haske cewa ba a kama Kanu da ke tafiya da fasfo din Birtaniya a cikin kasarta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel