2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa

  • Wata kungiyar mai wayar da kan al'umma ta shawarci Nnamdi Kanu da Sunday Igboho su fito takarar shugaban kasa a 2023
  • Kungiyar ta ce tsayawa takara shine hanyar da doka ta amince da shi na zama shugaba ba tayar da fitina ba
  • Kungiyar ta ce raba kasa ba zai zama alheri gare mu ba tana mai cewa duk wanda bai gamsu da wani abu a kasar ba ya nufi kotu

Wata kungiya mai suna 'Africa's New Dawn' ta bukaci ɗan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho da Nnamdi Kani, shugaba IPOB su yi watsi da gwagwarmayarsu su fito takarar shugaban kasa a 2023, rahoton The Guardian.

Shugaban kungiyar na kasa, Iluckukwu Chima, yayin da ya ke sanar da taron wayar da kan mutane da za su yi mai taken, 'One Love, One Nation, One President', a ranar Alhamis a Abuja ya ce zaman Nigeria a matsayin ƙasa guda ya fi alheri ga kowa.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'an Jamhuriyar Benin na yi wa Sunday Igboho da matarsa ‘yar kasar Jamus tambayoyi

2023: Ƙungiya Ta Shawarci Sunday Igboho Da Nnamdi Kanu Su Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa
Shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Yayin da gwamnatin Nigeriya ke tsare da Kanu, Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho yana hannun jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin bayan kama shi a filin tashin jirage na Bernardin tare da matarsa a hanyarsu na zuwa Jamus a daren ranar Litinin.

The Guardian ta ruwaito cewa Chima ya ce Nigeria kasa da ake kwatance da ita a nahiyar Afirka, yana mai cewa tarwatsa kasar zai janyo wa nahiyar matsala a duniya.

A cewar Chima:

"Nigeria ce ƙasar Afirka da duniya ta sani. Idan muka lalata Nigeria saboda ƙallubalen da muke fuskanta, wace kasar muke da shi? Rabuwa ba shine mafita ba. Maganin abin shine ƙaunar juna.
"Sai dai wasu suna son kafa gwamnatinsu. Igboho da Kanu na son kafa ƙasa a cikin wata ƙasa. Hakan ba zai iya faruwa ba domin Nigeria ta fi kowane mutum ɗaya.
"Duk wanda ke son kafa gwamnati ya yi haƙuri, ya gina jam'iyyar siyasa ya yi takara a 2023. A lokacin, masu zabe za su zabi abin da suke so. Kuɗin tsarin mulki ya ce a riƙa zabe bayan shekaru hudu kuma zaben zai fitar mana da shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan sanda sun fatattaki magoya bayan Sunday Igboho a wata jiha

A cewarsa, duk wanda bai gamsu da yadda ake tafiyar da kasar ba ya tafi kotu, yana mai cewa daukan doka a hannu ba ya kawo karshen rashin adalci.

Ya ce za su ratsa dukkan lungu da sako na kasar yayin gangamin su don wayar da mutane game da ƙarerayin da wasu masu muggun nufi ke watsawa don ɓata sunan Nigeria a gida da duniya baki daya.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164