Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

  • Sanata Ali Ndume na jihar Borno ya roki wata babbar kotun tarayya da ta tsame shi daga shari'ar Maina
  • Sanatan da ya tsayawa Abdulrasheed Maina har aka bada belinsa, ya roki kotun da ta bashi takardun kadarorinsa
  • Sai dai lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce kotun bata da hurumin sauraron wannan bukatar

Sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume a ranar Litinin ya bukaci babbar kotun tarayya dake zama a Abuja da su sahale masa zama wanda ya tsayawa Abdulrasheed Maina.

Idan zamu tuna, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa ya gurfana a gaban kotu bayan hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon ta zargesa kan badakalar kudi har naira biliyan biyu.

KU KARANTA: Fusatattun matasa sun kurmushe mutum 5 da ake zargin 'yan bindiga ne a Edo

Ndume na rokon kotu da ta sahale mishi tsayawa da yayi wa Maina
Ndume na rokon kotu da ta sahale mishi tsayawa da yayi wa Maina. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamna Bello Matawalle: Arewa ita ce matsalar kanta da kanta

Kara karanta wannan

Lauya ya ci alwashin maka Buhari a kotu idan ya hana 'yan Najeriya mallakar AK-47

Ndume, shugaban kwamitin sojoji na majalisar dattawa, yace baya son tsayawa Maina bayan da ya tsallake beli ya bar kasar baki daya, The Nation ta wallafa.

Ndume yace zai umarci lauyoyinsa da su fara kokarin cire shi daga alaka da shari'ar wacce ya saka hannu har aka bada belin Maina saboda a yanzu bai yarda da Maina ba.

A kotu ranar Litinin, lauyan Ndume, Marcel Oru, ya mika bukatar cire Ndume cikin shari'ar a rubuce kuma a mika masa takardun kadarorinsa da ya mikawa kotu.

Oru yace da farko za a iya cewa kotun bata da hurumin sauraron bukatar amma ganin cewa an kama Maina kuma yanzu yana gaban kotun, za a iya mika bukatar kuma ta saurara.

Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce kotun bata da hurumin sauraron wannan bukatar. Abubakar yayi kira ga kotun da ta soke bukatar tsame Ndume, The punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

A wani labari na daban, rundunar sojin saman Najeriya, NAF, ta musanta rahotannin dake yawo na hatsarin da jrigin samanta ya kara yi a Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata.

Akwai rahotannin dake yawo na cewa jirgin sojojin saman Najeriya wanda ya taso daga jihar Adamawa ya fadi a wani wuri a cikin jihar Kaduna.

Amma kuma yayin da aka tuntubi mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet, ya sanar da TheCable cewa babu wani hatsari da ya auku a Kaduna kamar yadda ya sanar da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng