Adalcin Shugaba Buhari da Saukin Kansa Yasa Na Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna

Adalcin Shugaba Buhari da Saukin Kansa Yasa Na Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna

  • Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River, ya bayyana yadda kyawawan halayen shugaba Buhari suka jawo hankalinsa
  • Gwamnan yace adalcin shugaba Buhari, kirkinsa da saukin kan da yake da shi ne suka sanya ya sauya sheka zuwa APC
  • Farfesa Ayade yace Buhari ya amince da kawo ziyara jihar Cross River, kuma zai kaddamar da ayyuka yayin ziyarar

Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya bayyana yadda kirki da saukin kan shugaba Buhari suka janyo hankalinsa ya koma APC, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Gwamna Ayade, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC kwanan nan, ya yi wannan jawabi ne a Daura, jihar Katsina.

Ayade na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC guda 12 da suka kaiwa shugaba Buhari ziyarar barka da sallah a mahaifarsa.

Gwamnan Cross River, Ben Ayade
Adalcin Shugaba Buhari da Saukin Kansa Yasa Na Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gwamnan ya ƙara da cewa shugaban ƙasa Buhari yana rayuwa ne fiye da tunani.

Gwamna Ayade yace: "Shugaba Buhari ne ya jawo hankalina zuwa APC ta hanyar saukin kansa, kirki, da adalci, halayen da ba'a cika samunsu a cikin mutane ba sai kaɗan."

Kara karanta wannan

Zan Jingine Siyasa a 2023 Domin In Koma Aikin Tallafawa Mutane, Gwamnan Arewa

"Misali, Buhari yana rayuwa a tsarin ginin gidansa tun shekaru 30 da suka wuce, kuma har yanzun ba'a kara komai a ginin gidan ba."

"Kasancewarsa shugaban ƙasar Najeriya na zangon mulki biyu kuma har yanzun yana cigaba da zama a wannan gidan abun a yaba masa ne, sannan bai faɗi son ransa ba wajen bayyana abinda ya mallaka."

Buhari zai kaddamar da ayyuka a Cross River

Gwamna Ayade ya bayyana cewa shugaba Buhari ya amince ya jagoranci kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinmu ta yi a Cross River zuwa watan Satumba.

Ya faɗi masana'antar noman cocoa da kuma kamfanin sarrafa shinkata a matsayin biyu daga cikin ayyukan da shugaba Buhari zai kaddamar yayin ziyarsa zuwa jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262