NPA: Sababbin bayanai su na fitowa game da sabanin Hadiza Bala Usman da Rotimi Amaechi
- Ana samun sabani tsakanin Hadiza Bala Usman da Rotimi Amaechi
- Kwamitin da zai binciki NPA ya na kawo maganar rashin yin biyayya
- Wannan kwamiti ya yi watsi da zargin da ake yi na karkatar da kudi
Rikicin cikin gidan da ake yi tsakanin shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na neman ya dauki wani irin yanayi.
Jaridar The Cable ta ce Ministan ya yi watsi da zargin da yake yi wa shugabar hukumar NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 a asusun gwamnati na CFR.
Wani cikin ‘yan kwamitin da aka kafa ya ya shaida wa jaridar cewa yanzu za su maida hankali ne a kan zargin Hadiza Bala Usman da laifin rashin kunya.
KU KARANTA: NLC ta ce za ta fara gagarumin yajin-aiki a Jihar Kaduna
“Muna kallon abubuwa biyu, na farko shugabar ta kasance ta na magana da shugaban kasa kai-tsaye, ta na watsi da ofishin mai girma Minista.” Inji Majiyar.
“Wannan babban rashin kunya ne da saba tsarin dokar aiki. Wannan ya isa ya sa a tsige ta.”
“Na biyu, Minista ya ba ta umarni ta dawo da kwangilolin Intel da aka dakatar ko aka kashe. Abin da ba ta sani ba shi ne, har shugaban kasa ya san da maganar.”
“Ba ta yi abin da aka umarce ta ba. Wannan saba wa maganar manya ne, ba ta fi karfin a horas da ita ba.”
KU KARANTA: Gwamnonin Kudu sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta canza salon rawanta
Jaridar ta ce babban hadimin shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya ki yin na’am da dawo da kwangilar Intel bayan hukumar NPA ta yi masa karin-bayani.
Ibrahim Gambari ya aika wa Ministan shari’a, Abubakar Malami, takarda ya na neman jin shawararsa, kuma ya tabbatar da cewa NPA ta fi Ministan gaskiya.
Wani aiki da kwamitin zai yi shi ne binciken kwangilolin da NPA ta bada, wanda a doka Ministan ne yake da hurumin sa hannu kafin a fitar da manyan kwangila.
Hadiza Bala Usman, shugabar NPA da aka dakatar ta yi wa Gwamna Nasir El-Rufai rakiya zuwa fadar sarkin Zazzau a Zariya, yayin da ake yin bikin karamar sallah.
Hajiya Hadiza Bala Usman ta wallafa hoton da ta dauka tare da El-Rufai inda ta bayyana shi a matsayin 'mai gidanta na har abada', a lokacin da aka dakatar da ita.
Asali: Legit.ng