Hadiza Bala Usman da aka dakatar, ta yi magana a kan alakarta da Dangote a hukumar NPA
- Hadiza Bala Usman ta musanya zargin cirewa Dangote kudin shigo da kaya
- Shugabar NPA da aka dakatar ta ce ba ta fifita kamfanin Dangote a Onne ba
- Usman tace gudun cunkoso ne ya sa aka kyale shigo da kaya ta tashar Onne
Shugabar hukumar NPA da aka dakatar, Hadiza Bala Usman, ta yi magana game da zarginta da ake yi na fifita kamfanin Dangote Group.
Hadiza Bala Usman ta musanya zargin cewa ta dauke wa kamfanin Dangote nauyin biyan da ake biya a tashar ruwan Onne da ke jihar Ribas.
The Cable ta ce a wani jawabi da Hadiza Bala Usman ta fitar a ranar Laraba, ta musanya wannan zargi.
KU KARANTA: NPA: Majalisa ta fara gayyato Hukumar EFCC da ICPC
A cewar Bala Usman, wannan zargi da ake jifan ta da shi na saba dokokin hukumar NPA ba gaskiya ba ne, neman a bata mata suna ne kurum.
A cewar Bala Usman wanda aka dakatar daga ofis a makonnin da suka wuce, an bi duk wasu ka’idojin aiki a lokacin da ta ke kan kujerar NPA.
Usman ta ce a wata takarda da NPA ta fitar a ranar 5 ga watan Fubrairun 2019, ta bada umarnin kowane kamfani ya rika biyan kudin shigo da kaya.
Daga cikin wadanda wannan umarni ya shafa tun a lokacin har da Messers Dangote Industries Limited.
KU KARANTA: Erdogan ya tuntubi Buhari domin ba mutanen Falasdina goyon-baya
Bayan Hadiza Bala Usman ta shiga ofis ne ta kawo sauyi a tashohin ruwa ta bada damar a rika shigo da kowane irin kaya ta tashar ruwan da ke Onne.
“Da wannan mataki, aka yanke cewa sai an duba kudin da za a karba a kan kowane kaya da aka shigo da su, akasin abin da aka saba yi a da.” Inji Usman.
Saboda a guje wa cinkoso a tashohin da ke Legas, aka ba kamfanin Dangote shawarar ya rika shigo da kayansa ta tashar Onne, ya biya kudin da ake biya.
Kwanakin baya kun samu labari cewa, an yi watsi da zargin batar da kudi, an koma zargin Shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da laifin rashin kunya
A cewar wani daga cikin 'yan kwamitin binciken, babban zunubin Bala Usman a lokacin da ta ke ofis, shi ne ta na yi wa Ministan sufuri rashin kunya karara.
Asali: Legit.ng