Hadiza Bala Usman: Ana cigaba da binciken NPA a kan zargin 'badakalar' Naira Biliyan 132 a 2018

Hadiza Bala Usman: Ana cigaba da binciken NPA a kan zargin 'badakalar' Naira Biliyan 132 a 2018

  • Mai binciken kudi a Gwamnati ya sake aika takarda zuwa ga hukumar NPA
  • Adolphus Aghughu ya na zargin hukumar da facaka da kusan Naira biliyan 90
  • Gwamnatin Tarayya ta ce NPA ta ki biyan harajin Naira Biliyan 44.1 a 2018

Ofishin mai binciken kudi a gwamnatin tarayya ya sake aika wasu takardu zuwa ga NPA, ya na zargin hukumar da rashin gaskiya wajen harka da kudi.

Jaridar Punch ta ce gwamnatin tarayya ta na zargin hukumar da yin aika-aika a shekarar 2018.

Daga cikin zargin da ke kan wuyan shugabanninn NPA akwai kin biyan hukumar FIRS harajin Naira biliyan 44.12 da yin facaka da Naira biliyan 88.23.

KU KARANTA: Ba ni da masaniyar an sallami Hadiza Bala Usman - Amaechi

Akwai haka-haka a kan kudin da aka kashe a 2018

Rahoton ya ce Adolphus Aghughu ya na so hukumar da ke kula da tashoshin ruwan kasar ta yi masa bayanin inda ta kai wannan kudi a shekarar ta 2018.

Binciken da gwamnatin ta yi ya nuna cewa NPA ta batar da Naira biliyan 409.17 da sunan sayen wasu kayan aiki, amma ba tare da an kawo takardun cinikin ba.

Har ila yau, Mista Aghughu ya na zargin NPA da rashin kokari wajen karbo bashin da ta ke bi.

Hukumar za kuma ta yi wa gwamnatin tarayya bayanin yadda aka kashe kusan Naira biliyan biyu a yarjejeniyar gidajen da ta shiga da Aso Savings & Loans Plc.

KU KARANTA: Maganar alakata da Dangote a hukumar NPA - Bala Usman

Hadiza Bala Usman
Hadiza Bala Usman da Shugaban kasa Hoto: www.dailypost.ng
Asali: UGC

An kashe N6.5bn wajen bada kwangiloli

Shugabannin NPA sun ce sun biya Naira biliyan 6.5 domin ayi wata kwangila, wanda yanzu gwamnati ta bukaci a fito da bayanin wadanda aka ba kwangilar.

Jaridar ta ce gwamnati na bukatar sanin kamfanin da aka ba kwagila, yanayin kwangilar, kudin da aka ware, abin da aka fitar, da inda aka kwana a aikin a yanzu.

An umarci NPA ta maida wasu Naira biliyan 2.33 a asusun gwamnati. An boye kudi ne a banki tun 2017 bayan EFCC ta shiga maganar wani sabani da aka samu.

Kwanaki kun ji cewa ana samun sabani tsakanin Hadiza Bala Usman da Rotimi Amaechi inda kwamitin da zai binciki NPA ya kawo maganar rashin biyayya.

Ministan sufurin ya yi watsi da zargin da ake yi wa shugabar hukumar NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 a asusun gwamnatin tarayya a lokacin da ta ke ofis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel