'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 6 Yayin Da Suka Afkawa Wasu Gidaje a Abuja
- Yan bindiga sun kai hari Tungan-Maje a birnin tarayya Abuja sun sace mutum shida
- Hakimin Tungan-Maje, Alhaji Hussaini Barde ya tabbatar da harin yana mai kira ga jami'an tsaro su taimaka musu
- Wasu mazauna garin sun bayyana yadda yan bindigan suka raba kansu kashi uku kafin suka shiga gidan mutane
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane shida mazauna Tungan-Maje a ƙaramar hukumar Gwagwalada ta Abuja.
Daily Trust ta ruwaito cewa masu garkuwar da suka afka unguwar da yawa sun shiga wasu gidaje a Anguwar Dabiri da Anguwar Sarki a yankin.
DUBA WANNAN: Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah
Wani shaidan ganin ido ya ce masu garkuwar sun raba kansu gida uku kafin shiga gidaje uku a yankin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wasu yan bindiga sun yi ta harbe-harbe a iska kafin su tafi da wadanda suka sace.
Ya ce:
"Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun tsaya a wasu wurare a unguwar yayin da sauran suka shiga gidajen mutane suka fito da su suka nufi daji."
Hakimin Tungan-Maje, Alhaji Hussaini Barde, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce mutane shida aka sace.
KU KARANTA: Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa
Ya ce:
"Masu garkuwa da mutane sun adabi mutane ne na a Tungan-Maje. Tun daga Satumban bara an kawo mana hari sau tara."
Ya kuma yi kira ga jami'an tsaro su kawo ma mutanensa ɗauki yana mai cewa isassun jami'an tsaron za su iya magance matsalar.
Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ba.
'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Jiha a Gidanta
A wani labri daban, wasu Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace mahaifiyar sakataren gwamnatin jihar Bayelsa, Mrs Betinah Benson.
The Punch ta ruwaito cewa wadanda suka sace ta sun taho ne sanye da kaki irin ta sojoji.
An gano cewa an sace mahaifiyar Konbowei Benson a daren ranar Talata a gidansa da ke tsohuwar rukunin gidajen assembly ta Yenagoa.
Asali: Legit.ng