Idan ka biyewa Yariman Bakura zai kai ka ruwa, AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa

Idan ka biyewa Yariman Bakura zai kai ka ruwa, AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa

  • Da alamun har yanzu akwai rikici a cikin gidan APC a jihar Zamfara
  • Tsohon gwamna Yari ya yiwa Sanata Sani Yarima wankin babban bargo
  • Ya baiwa gwamna Matawalle shawara yayi hattara da yan siyasan dake zagaye da shi

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari, ya soki matakin da shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya dauka na rusa shugabannin jam'iyyar na jihar.

Yari, wanda ya yi jawabi ga mabiyansa a gidansa dake Talata-Mafara ranar Juma'a yayi kira ga gwamna Matawalle yayi hattara da wasu yan siyasa dake zagaye da shi saboda zasu batar da shi daga kan hanya.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga mambobin APC a jihar su kwantar da hankalinsu saboda mulki zai dawo hannunsu a 2023, rahoton Punch.

Yace:

"Wasu na fadin zan fita daga APC. Ina daya daga cikin mutum 10 da suka kafa jam'iyyar, ba zan taba fita daga cikinta ba, duk abinda zai faru."

Kara karanta wannan

Ku tarwatsa bangaren Yari na APC a Zamfara, Shinkafi yayi kira ga Buni da IGP

"Shirye muke mu fuskanci Yarima. Ina daya daga cikin wadanda suka taimaka masa a siyasarsa. Mai Mala Buni yayi kuskure na rusa kwamitin rikon kwaryam Zamfara."

AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa
Idan ka biyewa Yariman Bakura zai kai ka ruwa, AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da magabacinsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kara da cewa:

"Yarima yayi iyakan kokarinsa don ganin na koma PDP amma naki."
"Idan ka biyewa Yarima zai batar da kai.N1.7bn aka baiwa Yarima da wasu lokacin taron gangamin hadin gambizan APC."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng