Buhari ya tura tawaga gidan Sarkin Bichi don sa ranar auren 'dansa Yusuf

Buhari ya tura tawaga gidan Sarkin Bichi don sa ranar auren 'dansa Yusuf

  • Za'a sa ranar auren 'dan gidan Buhari da 'yar gidan Sarki Nasir Ado Bayero
  • Masoyan biyu sun yi karatunsu a kasar Birtaniya
  • Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan abu

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika tawagar wakilansa domin ganawa da iyalan Sarkin Bichi kan sa ranar daurin auren 'dansa, Yusuf Buhari, da Zahra Bayero.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan tawagar da Buhari ya tura ta hada da gwamnoni, Ministoci, da Dirakta Janar da hukumar DSS, Yusuf Bichi.

An tattaro cewa tuni wasu sun dira jihar Kano da kayayyakin sa rana irinsu goro, da sauransu.

Hakazalika an shirya ganawar tawagar da dattijon gidan Bayero, Idris Bayero, da Sarkin Kano, Aminu Bayero, ranar Lahadi.

Za'a sa ranar auren 'dansa Yusuf
Buhari ya tura tawaga gidan Sarkin Bichi don sa ranar auren 'dansa Yusuf Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

A watan Maris mun kawo muku labarin cewa Yusuf Buhari, dan gidan shugaban kasa Muhammadu, na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, rahoton Daily Nigerian.

Zahra Bayero a lokacin tana karatun ilmin zanen gine-gine a kasar Birtaniya yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami'ar Surrey, Guildford, a Birtaniya.

Wata Majiya ta ce da tuni an yi bikin amma saboda rashin kasancewar mahaifiyar Yusuf, hajiya Aisha Buhari, wacce ta dawo daga Dubai inda ta kwashe watanni shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel