Tinubu ya hana Fasto Bakare zama Mataimakin Buhari a zaben 2015, ya kakabo Osinbajo

Tinubu ya hana Fasto Bakare zama Mataimakin Buhari a zaben 2015, ya kakabo Osinbajo

  • Sanata Rufai Hanga ya bada labarin abin da ya faru lokacin zabukan 2011 da 2015
  • Tsohon abokin tafiyar na Buhari ya ce Bola Tinubu ya hana a tafi da Tunde Bakare
  • Hanga yake cewa Bola Tinubu ne ya kawo Osinbajo ya zama Mataimakin Buhari

Jigon tsohuwar jam’iyyar CPC, Sanata Rufai Hanga ya ce Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya tare Tunde Bakare, ya hana shi yin takara da Muhammadu Buhari.

Sanata Rufai Hanga ya bayyana wannan ne yayin da ya yi wata tattauna wa da jaridar Daily Trust.

Babban ‘dan siyasar ya ke cewa Muhammadu Buhari ya so ne ya yi takarar shugaban kasa tare da Fasto Tunde Bakare kamar yadda suka tsaya tare a zaben 2011.

KU KARANTA: Buhari ya ba ‘Yan Najeriya kunya da ya samu mulki - Bakare

A karshe dai jigon na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ki yarda da wannan batun, ya bada shawarar a hada Muhammadu Buhari ya yi takara da Farfesa Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

“Akwai lokacin da muke so mu hadu da jam’iyyar Tinubu ta ACN gabanin zaben 2011.”
“Wadannan mutane sun je sun fada wa Buhari cewa ka da ya sake ya karbi komai daga wurin Tinubu.”
“Maimakon Buhari ya dauki abokin takara, El-Rufai ya kawo masa Tunde Bakare. Wannan ya fusata Tinubu a lokacin, sai ya janye, daga nan Buhari ya sha kasa.
Buhari da Fasto Bakare
Shugaban kasa Buhari da Bakare Hoto: punchng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Bakare: Ban ce Buhari ya kunyata 'yan Najeriya ba

“Sai abubuwa suka tafi a haka. Amma mun samu kuri’u miliyan 12. Daga nan sai mutane su ka fara cewa lallai ya kamata a hada-kai, ayi tafiya tare da Buhari.”
“Daga baya Tinubu ya zo wajen Buhari, ya ce, “’Yallabai, an fada maka wasu abubuwa a game da ni. Na yarda ni ba mutumin kirki ba ne, amma za mu ba ka nasara.”

Sanata Rufai Hanga ya ce Buhari ya biye wa Bola Tinubu a zaben 2015, aka hada-kai. A wancan lokaci, an sake kawo Bakare, amma Tinubu ya dage a kan Yemi Osinbajo.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Yari ya ce wasu 'Yan siyasan Arewa na kokarin hana shi zama Shugaban APC

Kun san Bakare ya tsaya takara a matsayin mataimakin shugaban kasa da Muhammadu Buhari, amma ba su yi nasara ba. A 2015 ne Buhari da Yemi Osinbajo suka ci zabe.

A kwanakin baya ne aka ji Bakare ya na bayyana burinsa na karbar mulki idan Buhari ya sauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng