Buhari ya ba ‘Yan Najeriya kunya - Mulki na canza mutane inji Fasto Bakare

Buhari ya ba ‘Yan Najeriya kunya - Mulki na canza mutane inji Fasto Bakare

- Tunde Bakare ya bayyana cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza

- Babban limamin cocin Citadel Global Community yace an ba kowa kunya

- Bakare ya bayyana wannan ne a yayin da Dele Momodu ya tattauna da shi

Tunde Bakare, babban limamin cocin Citadel Global Community wanda aka fi sani da Latter Rain Assembly, ya koka da gwamnatin APC mai-ci.

Fasto Tunde Bakare ya fito ya na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba jama’a kunya.

Tunde Bakare ya bayyana wannan ne lokacin da ya ke hira da Dele Momodu, ‘dan jarida kuma mawallafin mujallar Ovation a shafinsa na Instagram.

The Cable ta rahoto cewa an yi wannan hira ta kafar yanar gizo da Bakare ne a ranar Talata, inda ya yi magana game da shugabanci da hadin-kan kasa.

KU KARANTA: Ina son in zama Magajin Buhari a 2023 - Bakare

Fasto Bakare ya ce kiran a raba Najeriya ‘ya na kara karfi’ a yanzu, don haka ya yi kira a zaunar da kasar nan lafiya, ya ce ya na sa ran a kai ga ci wata rana.

“Zai fi kyau Najeriya ta tsaya a dunkule. Idan mu ka duba ainihin yadda mu ka hadu, mu koma 1960 da 1963, duk da haka za mu iya cigaba da zama tare."

“Maganar gaskiya ita ce Buhari ya dauki wasu matakai na dabam. A iyaka sani na, shi ne dai shugaban kasar nan, wasu na tambaya ta ko wani ne dabam.”

Bakare yake cewa idan aka yi masa wannan tambaya, sai ya ce da wani ne, da Duniya ta gane.

KU KARANTA: Bakare ya ajiye sanayya, ya soki Gwamnatin Buhari

Buhari ya ba ‘Yan Najeriya kunya - Mulki na canza mutane inji Fasto Bakare
Fasto Tunde Bakare Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: Twitter

Ya cigaba da cewa: “Mulki na canza mutane. Ko kujerar mulki ya canza shi, ko ya na amfani da damar da ya samu da kyau? Shi zai amsa wannan tambaya.”

Tsohon abokin tafiyar Buhari ya ce “Ko ma dai wani buri ne ya sa aka kawo shugaba Buhari, ba a cinma wannan manufa ba, saboda haka ko ina takaici ake yi."

Kwanakin baya kun ji cewa shugaban cocin na Latter Rain Assembly, Tunde Bakare ya jero wasu mutane da ya bayyana a matsayin ainihin makiyan Najeriya.

Babban Faston ya yi jawabin ne yayinda yake bayyana ra’ayinsa a kan halin da kasar ke ciki. A cewarsa wadannan ba kowa ba ne sai masu sace dukiyar kasa.

Bakare ya ce ana samun wadannan miyagun mutane a kowane mataki na gwamnati a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel