Tsohon Gwamna Yari ya ce wasu 'Yan siyasan Arewa na kokarin hana shi zama Shugaban APC
- Alhaji Abdulaziz Yari ya dage a kan bakarsa na zama Shugaban APC na kasa
- Yari ya ce akwai ‘Yan siyasa na Arewa da su ke neman ganin bai kai labari ba
- Tsohonn Gwamnan ya yi ikirarin ya na da abin da ake nema a rike a Jam’iyya
Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya ce babu wani yunkuri da za a iya yi domin a hana shi neman takarar shugaban jam’iyyar APC.
Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranarr Asabar, 18 ga watan Yuli, 2021, Abdulaziz Yari yace ko ana ha maza-ha mata, dole sai ya nemi kujerar.
Abdulaziz Yari ya tabbatar da wannan ne a lokacin da ya yi hira da manema labarai a garin Abuja.
KU KARANTA: Siyasar Zamfara: AbdulAziz Yari yayi kaca-kaca da Yariman-Bakura
Akwai masu neman hana ni kai labari
Yari ya ke cewa wasu tsofaffin abokan aikinsa da manyan Arewa maso yamma da suke tare a siyasa, suna kokarin ganin bai cin ma burin da ya sa a gaba ba.
“Wani ya fada mani, wasu abokan tafiya ta, da tsofaffin abokan aiki na, suna da wadanda su ke so su samu kujerar shugaban jam’iyya da mataimakinsa, idan aka kawo kujerar Arewa maso yamma.”
“Za su hada-kai, su taru domin ganin sun ci karfin Abdulaziz Yari.”
“Idan Ubangiji ya tsara, haka zai faru. Mutane za su iya yin duk dabarun da za suyi, suyi ta lissafinsu, amma ba za su yi nasara ba.”
KU KARANTA: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari
Sun san na dace in rike shugabancin APC
“Kuma na san wannan; na cancanci in jagoranci wannan jam’iyya, kuma sun san abin da zan iya.”
Daily Trust ta rahoto Abdulaziz Yari ya na cewa mukaman da ya rike a jam’iyya da gwamnatin jiha, za su taimaka masa idan ya zama shugaban jam’iyyar APC.
Yari ya ce ya yi sakatare da shugaban jam’iyya a jiha, sannan ya zama ‘dan majalisar tarayya, kafin ya yi gwamna, kuma har ya rike shugaban duka gwamnoni.
‘Dan siyasar ya ce masu harin kujerar mataimakin shugaban kasa bai kamata su rufe idanu, su rika adawa da shi wajen ganin ya zama shugaban APC na kasa ba.
A makon da ya gabata ne, aka ji Sanata Rufai Hanga ya na cewa Ali Modu Sheriff ne kadai gwamnan da ya ba Muhammadu Buhari kudi a lokacin zaben 2007.
Duk da ANPP ta na da Gwamnoni a wasu jihohin kasar nan a 2007, amma Gwamnan Bornon ne kadai ya iya taimakon Buhari a wancan lokaci a cewar Rufai Hanga.
Asali: Legit.ng