Ban ce Buhari ya kunyata 'yan Najeriya ba, Fasto Tunde Bakare
- A ranar Alhamis Fasto Tunde Bakare wanda aka fi Sani da Latter Rain Assembly, ya musanta cewa Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya
- Bakare ya musanta kalamansa ne lokacin da ake tambayarsa akan kalaman da yayi akan Buhari inda yace sharrin gidajen jaridu ne
- Bakare ya zage yana yabon Buhari har yana cewa hawar Buhari kan mulkin Najeriya a 2015 rahama ne ga mutane masu yawan gaske
Fasto Tunde Bakare, mai kulawa da cocin Citadel Global Community, wanda a baya ake kiranshi da Latter Rain Assembly, ya musanta ikirarin cewa Buhari ya ci amanar 'yan Najeriya a ranar Alhamis.
Ya kuma bayyana ra'ayinsa akan yadda Sunday Igboho ya shiga al'amarin kisan makiyaya, Vanguard ta wallafa.
Faston ya yi wannan musun ne a Arise TV, bayan an tambaye shi akan hirarsa da mawallafin Ovation Magazine, Dele Momodu, a Instagram.
KU KARANTA: Bidiyon magidanci ya saki matarsa bayan mahaifiyarta ta hana shi ganin 'ya'yan shi
Bakare ya musanta kalamansa, inda yace lallai 'yan jarida sun kirkiri hakan ne don su samu jaridunsu su yi kasuwa.
Kamar yadda Bakare yace: "Gidajen jaridun sun kirkiri kalaman ne don su samu jaridunsu tayi kasuwa. Amma tabbas ban fadi hakan ba."
Ya ce: "Hawan Buhari mulki a 2015 rahama ne ga mutane da dama. Duk da ana tsaka da rikici, fadace-fadace da sauran abubuwa, mutane sun cika sanya buri, wadanda da dama daga cikin burikansu basu cika ba.
"Lallai jaridu suna wallafa kalaman da za su janyo hankulan jama'a wurinsu ne. Amma maganar gaskiya, shin ya ci amanar 'yan Najeriya? Kullum muna ganin a labarai mutane suna bayyana takaicinsu da nadamarsu akan mulkin nan.
"Amma hakan ba ya nufin babu wani abin kirkin da wannan mulkin ya samar."
KU KARANTA: El-Rufai ya kushe yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga wasu sassan kasar nan
A wani labari na daban, wata gagarumar gobara ta tashi a kasuwar tippe da ke Gwarinpa a Abuja. An gano cewa mutum 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka samu raunika a ranar Alhamis.
Gobarar ta fara ne da daya daga cikin shagunan wanda ya shafa wasu a cikin sa'o'i biyu kafin isowar 'yan kwana-kwana.
Wani ganau ya sanar da The Punch cewa masu kashe gobarar basu iso ba sai wurin karfe 2 na dare bayan kasuwar ta shafe da wuta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng