Masarautar Zazzau Ta Soke Bikin Hawan Salla Saboda Cutar Korona

Masarautar Zazzau Ta Soke Bikin Hawan Salla Saboda Cutar Korona

  • Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan na babbar sallah saboda kare jama'a daga cutar COVID19
  • Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli, shine ya bayyana haka ga manema labarai rananr Litinin
  • Yayi kira ga iyaye da su sanya ido kan yayansu yayin da al'umma zasu fara shagulgulan sallah

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli, ya sanar da soke bikin hawa na babbar sallah (eid-el-kabir) a Zariya domin biyayya ga ƙa'idojin kare yaɗuwar COVID19, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Abin Tausayi: Yadda Jami'an NIS Suka Kuɓutar da Wani Yaro da Aka Sace a Cikin Akwatin Gawa

Sarkin ya bada wannan sanarwa ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadarsa dake Zariya ranar Litinin.

A cewar sarkin, majalisarsa ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan sake ɓarkewar annobar COVID19 a karo na uku, kuma mafi yawancin masarautu sun soke bikin hawa.

Yace: "Mun soke hawan sallah ne domin kare lafiyar al'ummar mu yayin da annobar COVID19 ta sake ɓarkewa."

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Sarkin.Zazzau, Ahmed Bamalli
Masarautar Zazzau Ta Soke Bikin Hawan Salla Saboda Cutar Korona Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sarki yayi kira ga gwamnati

Sarkin ya yi Allah wadai da ƙalubalen rayuwa da al'ummar da yake jagoranta suke ciki, saboda haka yayi kira ga gwamnati a dukkan mataki da ta ɗauki matakin magance matsalolin.

Yace: "Matuƙar aka magance matsalolin rayuwa da mutane ke ciki to za'a samu sauki a ɓangaren tsaro."

Ya kuma yaba wa shugabannin addinai bisa jajircewarsu wajen addu'a domim samun zaman lafiya a yankin masarautarsa.

KARANTA ANAN: Babbar Sallah: Ku Kara Hakuri Yayin da Muke Kokarin Inganta Rayuwarku, Shugaba Buhari Ga Yan Najeriya

Bamalli ya yabawa gwamnatin Kaduna

Ahmed Bamalli ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna bisa ɗumbin ayyukan cigaba da ta gudanar a yankin masarautarsa dama jiha baki ɗaya.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara samar da ruwan sha a Zariya domin samun isasshen ruwa ga al'umma.

Sarkin yayi kira ga iyaye da su kula da yayan su yayin da al'ummar musulmai ke shirin bikin babbar sallah.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

A wani labarin kuma DSS Ta Hana Nnamdi Kanu Sanya Hannu a Takardar Taimakon Burtaniya

Hukumar DSS ta hana Nnamdi Kanu ya sanya hannu a takardar da Burtaniya ta aiko masa.

Ɗaya daga cikin lauyoyin shugaban tawaren, Aloy Ejimakor, shine ya bayyana haka ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel