Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano

  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane 225 da ake zargi da laifi
  • Wadanda aka kama sun hada da yan fashi, masu garkuwa, barayin mota, masu kwacen waya da sauransu
  • Rundunar yan sandan ta yi nasarar kwato muggan makamai daga hannunsu kuma tana zurfafa bincike kafin a kai su kotu

Rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama mutane 225 da ake zargi da aikata miyagun laifuka daban-daban tsakanin rana 1 ga watan Yuni zuwa 16 ga watan Yulin 2021, rahoton Premium Times.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi.

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano
Wukake, barandami, takkuba da muggan makamai da yan sanda suka kama a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ku Bar Gari Ko Mu Aurar Da Ku: Ciyaman Ya Bawa Karuwai Wa’adin Kwana 30 a Jigawa

Ya ce cikin wadanda aka kama akwai mutum 21 da ake zargi da fashi da makami da bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane. Sauran sun hada da mutum 23 da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne, 18 masu zamba, biyar barayin motocci, 11 barayin shanu sai yan daba 140.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Dan Kasar Denmark da ya yi zanen batanci ga Annabi ya koma ga Allah

Mr Kiyawa ya ce a ranar 7 ga watan Yuli wai Ado Shuaibu mazaunin kauyen Malaku a karamar hukumar Doguwa ya kira wani Yakubu Abdu na kauyen Shere ya nemi ya biya miliyan biyu ko a sace shi.

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano
Muggan makamai da yan sanda suka kwace hannun bata gari a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

"Bayan samun rahoton, kwamishinan yan sandan Kano, CP Sama'ila Shuaibu Dikko, fsi, ya umurci tawagar yan sanda karkashin jagorancin CSP Bala Shuaibu, DPO na Doguwa su dauki mataki.
"Tawagar nan take suka shiga aiki suka yi kwantar bauna a wurin da aka shirya bada kudin suka yi nasarar kama wani Ado Shuaibu dan shekara 24 mazaunin Kauyen Maraku a karamar hukumar Doguwa na jihar Kano.
"An harbi wanda ake zargin a kafarsa na dama a yayin da ya yi kokarin tserewa, an garzaya da shi babban asibitin Doguwa an masa magani. An kwato bindiga pistol a hannunsa da waya Tecno da sim kad da yayi amfani da shi wurin yi wa wanda ya yi korafin barazana, adda da leda (wanda zai saka kudin fansan a ciki.)"

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano
Takubba, Adda, Gwafa, Almakashi da sauran muggan makamai da ya sanda suka kama a Kano: Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Kakakin yan sandan ya kara da cewa a ranar 2 ga watan Yuli, tawagar yan sanda yayin sintiri a dajin Falgore karamar hukumar Tudun Wada sun kama wani Abdulrahman Usman na kauyen Kurmi a karamar hukumar Soba na jihar Kaduna da wasu mutane 5 da suka kai hari rugar makiyaya a dajin.

KU KARANTA: Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

"Makiyayan sun dakile harin suka yi wa maharin rauni, sannan daga bisani yan sanda suka kama shi dauke da pistol na gargajiya," in ji shi.

An garzaya da shi asibiti aka masa magani sannan daga bisani ya tona asirin abokansa da dama da suke aikata laifuka tare. Ya kuma amsa cewa sun aikata fashi da makami da garkuwa da mutane sau da dama.

Kama wadanda ake zargi da fashi da makami

Kara karanta wannan

Dubun Abdullahi Bummi shugaban 'yan bindigan Jigawa ta cika, an ceto tsohuwa 1

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano
Wanda aka kama kan zargi fashi da makami a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Kakakin yan sandan ya ce an kama wani Rabiu Danjuma da aka fi sani da Rabiu Duty; Suleiman Idris, wanda ake fi sani da Magu; Abel Patrick, Wisdom John da Stephen Sedani.

Ya ce wadanda ake zargin sun kai hari gidan wani Sahaisu Abdullahi mazaunin kauyen Gunduwawa a karamar hukumar Gezawa suka sace masa mitarsa, Honda Accord da Talabijin.

An kuma kama wani Abdullahi Ibrahim na Gidan Kankara Quaters a Kano wanda ya hada baki da wani Bashir Bashir wanda aka fi sani da Sahabi; suka kaiwa daliban FCE Zaria hari suka kwace musu wayoyin salula da kudinsu ya kai N200,000.

"Yan sandan sun kuma kama wani Khalifa Muhammad, Ahmed Muhammad da Halifa Ahmed duk mazauna kurna Quaters dauke da bindigan roba, kakin sojoji, wayoyin salula, kudi da wasu kayayyaki.
"Yayin bincike sun amsa cewa sun yi wa wata Hajiya Umma Musa fashi sun mata rauni. Ana cigaba da bincike," in ji shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

Wadanda ake zargi da satar wayan salula

Hotunan Bindigu, Makamai Da Ƙwayoyi Da Ƴan Sanda Suka Ƙwato Hannun Ƴan Fashi Da Masu Garkuwa 225 a Kano
Muggan kwayoyi da makamai da aka kama hannun masu kwacen waya da kudade a Kano. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Kazalika, an kuma kama mutane 37 da ake zargi masu kwacen waya ne a Kogar Dan'agundi.

"A ranar 04/06/2021 misalin karfe 7 a yamma, yan sanda sun samu rahoton cewa wasu bata gari dauke da adduna, wukake da wasu muggan makamai suna tare mutane a Kofar Dan'agundi suna kwace musu wayoyi, kudade da wasu kayayyakin.
"Nan take kwamishinan yan sandan Kano, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko, fsi, ya tra tawaga karkashin jagorancin SP Bashir Gwadabe domin a kamo su."

Da isarsu, bata garin sunyi kokarin kai musu hari amma yan sandan suka yi galaba kansu, hakan yasa suka bar makamansu suka tsunduma cikin kududufin Bakar Lamba a Kofar Dan Agundi amma yan sandan suka zagaye kududufin suka kama su.

An kama kimanin mutum 37 daga cikinsu tare da kwato makamai da muggan kwayoyi da suke dauke da su.

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

Kara karanta wannan

'Ƴan Sanda Sun Kama Mai Sayarwa Ƴan IPOB Miyagun Ƙwayoyi

A wani labarin daban, rundunar ƴan sanda na jihar Kano ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda na bogi a wani otel a birnin Kano, The Punch ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Haruna ya ce an kama wanda ake zargin, wani Mohammed Aliyu mazaunin Mariri Hotoro Quarters bayan ya gabatar da kansa a matsayin ACP a wani otel a Kano ya kuma nemi a bashi ɗaki ya sauki baƙinsa da ke zuwa daga Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel