Daga Karshe: Dan Kasar Denmark da ya yi zanen batanci ga Annabi ya koma ga Allah

Daga Karshe: Dan Kasar Denmark da ya yi zanen batanci ga Annabi ya koma ga Allah

  • Wani bature mai zanen shagube ya mutu bayan shekaru yana aikin zane-zane a kasar Denmark
  • Mutumin ya sanu ne lokacin da ya yi wani zanen batanci ga Annabi Muhammadu SAW
  • Kafin mutuwarsa, ya kasance a kebabben wuri saboda barazanar da yake fuskanta na kisa

Mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na batanci Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo cece-kuce, ya koma ga Allah. Ya mutu yana da shekarun 84, BBC Hausa ta ruwaito.

An wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutukar da Musulmi masu kishin muslunci suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama na Musulmai.

A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya karasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar 'yan sanda.

KARANTA WANNAN: Shugaban hafsan soji ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankali zai magance tsaro

Daga Karshe: Dan Kasar Denmark da ya yi zanen batanci ga Annabi ya koma ga Allah
Kurt Westergaard | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.

Matasan Sakkwato sun mamaye fadar Sarkin Musulmi akan kalaman batanci ga Annabi

Wasu matasa a Sakkwato sun mamaye fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, suna neman a kama tare da gurfanar da wani Isma'ila Sani Isah na yankin Gobirawa.

Matasan dai suna zargin Isah da sanya kalaman batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a dandalinshi na sada zumunta ran laraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya yi furucin ne domin nuna rashin amincewarsa da rashin samun aikin karamar hukuma.

A cikin wallafar da aka ce yayi kamar yadda majiyarmu ta kawo, Isah ya zargi wani mutum a yankinsu da hana shi aikin duk da matsalar kudi da yake fuskanta.

Matasan wadanda ke dauke da kwalayen sanarwa inda wasunsu ke dauke da rubutu kamar "Muna kira ga majalisar masarautar ta dauki matakin da ya dace kan mai laifin" da kuma "dole ne Isma'il ya mutu" da sauransu sun kutsa cikin fadar da misalin karfe 5:00 na yamma.

KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

Hukunta mutane kan laifin batanci ga Annabi abin damuwa ne, Amurka

A wani labarin, kasar Amurka ta bayyana damuwarta kan yadda kotuna a Najeriya ke cigaba da hukunta masu laifin batanci ga Annabi, ta hanyar jefasu kurkuku da yanke musu hukuncin kisa.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rahoton yancin addini na 2020, rahoton Punch.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya har yanzu bata hukunta wadanda suka hallaka mambobin kungiyar Shi'a da aka yiwa kisan gilla a shekarar 2015 ba amma tana hukunci masu laifin batanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel