Ku Bar Gari Ko Mu Aurar Da Ku: Ciyaman Ya Bawa Karuwai Wa’adin Kwana 30 a Jigawa

Ku Bar Gari Ko Mu Aurar Da Ku: Ciyaman Ya Bawa Karuwai Wa’adin Kwana 30 a Jigawa

  • Karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa ta dau zafi kan yunkurin fatattakar mata masu zaman kansu a jihar
  • Zaharadeen Abubakar, shugaban karamar hukumar ya bawa karuwan wa'adin kwana 30 su bar garin ko su fito da miji a yi musu aure
  • Har wa yau, Abubakar ya bada umurnin a rufe dukkan gidajen casu da wuraren shan giya da ke karamar hukumar ta Gwaram

Karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa ta dauki sabbin matakai a yakin da ta ke yi da mata masu zaman kansu inda ta basu wa'adin kwanaki 30 su fice daga yankin ko kuma a aurar da su, Daily Trust ta ruwaito.

Matan masu zaman kansu wadanda ba yan asalin karamar hukumar bane za a mayar da su garuruwansu na asali.

Ku Bar Gari Ko Kuyi Aure: Shugaban Karamar Hukuma Ya Bawa Karuwai Wa’adin Kwana 30
Taswirar Jihar Jigawa: Hoto: The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Ku kashe shi da zarar an sake shi' - Sheikh Yabo ya yi fatawa kan wanda ya yi wa Annabi ɓatanci a Sokoto

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa

Rahoton na Daily Trust ya kuma ce wadanda kuma yan gari ne da ke da niyyar tuba su sauya sana'arsu su tabbata sun shirya yin aure.

An umurci su mika sunanayensu da na mazan da za su aure su kafin wa'adin da aka basu na kwanaki 30 ta cika.

Shugaban karamar hukumar Gwaram, Zaharadden Abubakar ya ce:

"karamar hukumar a shirye ta ke ta dauki nauyin aurar da mata masu zaman kansu yan asalin karamar hukumar idan sun shirya su bar sana'ar."

KU KARANTA: IPOB Ta Bayyana Gwamnoni 2 Da Minista Da Suka Ɗauki Nauyin Kamo Nnamdi Kanu

A wani taro da aka yi a garin Sara, wani fitaccen kasuwar da ke ci mako-mako a karamar hukumar, Abubakar ya umurci dukkan mata masu zaman kansu da ke yankin su mika wa karamar hukuma sunayen mazan da ke harka da su kafin karshen wa'adin.

Ya kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen casu da gidajen shan giya a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina

Abubakar ya ce an dauki matakin ne domin magance ayyukan alfasha a karamar hukumar.

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

A wani labarin daban, kun ji cewa manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel