Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno

Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno

- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya dauki manoma 6,111 a shirin manoma na kananan hukumomi 10 na jihar

- Kwamishinan aikin gona na jihar, Bukar Talba, ya bayyana hakan a jawabin da yayi wa manema labarai a Maiduguri

- Talba ya ce, sakamakon aikin 'yan ta'adda, akwai yuwuwar tabarbarewar tsaron abinci a jihar

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya dauki manoma 6,111 aiki a babban shirin manoma a fadin kananan hukumomi 10 na jihar don hana rashin abinci a nan gaba.

Kwamishinan aikin gona, Bukar Talba, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a Maiduguri a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Borno ta kafa kwamitin don kafa shirin inganta noma da samar da abinci a jihar.

Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno
Gwamna Zulum ya dauki manoma 6,111 aiki a Borno Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Kamar yadda Talba yace, sabbin manoman za su yi aiki don fadada ayyukan samar da abinci. Za su yi aiki a matsayin mafarauta da kuma jami'an tsaron farar hula yayin da suke gonakin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Ondo yayinda ake shirin tsige matainakin gwamna

Ya ce sakamakon ayyukan 'yan ta'adda, an samu karancin manoma domin wasu sun yi gudun hijira kuma hakan babbar barazana ne ga tsaron abinci a jihar.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar na kokarin habbaka tattalin arzikin jihar ta hanyar bada fifiko a bangaren noma da kiwo.

A wani bangare, a kokarin gwamnatin jihar na yakar ayyukan 'yan ta'adda, Gwamna Babagana Umaru Zulum ya kwace gidaje 100 da aka gina a garin Bama.

Gwamnan ya bada gidajen a ranar Litinin 8 ga watan Yuni ga 'yan gudun hijira a karamar hukumar Bama.

A wani labarin na daban, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya kushe gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa.

Ya bayyana gwamnatin da mafi munin gwamnati da aka taba yi a tarihin kasar nan.

A yayin jawabinsa a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya, Dalung ya ce duk da makuden kudin da ake warewa tsaro, babu abinda ya sauya a kan kashe rayukan 'yan Najeriya tamkar dabbobi.

A yayin bayyana matsayarsa a harshen Hausa, Dalung wanda ya yi minista tsakanin 2015 zuwa 2019, ya bayyana mulkin shugaba Buhari da mafi munin mulki a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng