Buhari ya ki taba sisin kobo cikin miliyoyin da Surukinsa ya ba shi a matsayin gudumuwar zabe
- Rufai Hanga ya bada labarin abin da ya faru a lokacin da ake tafiyar Jam’iyyar ANPP
- Sanata Hanga yace a zaben 2007, Ali Modu Sheriff ne kadai ya ba Buhari gudumuwa
- Sauran gwamnonin ANPP sun dunkule hannuwansu, a karshe Jam’iyyar ta sha kashi
Rufai Hanga, daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar CPC a Najeriya, ya bada labarin yadda Muhammadu Buhari ya ki karbar kudin Ali Modu Sheriff.
A wata hira ta musamman da Daily Trust ta yi da Sanata Rufai Hanga, ya bayyana cewa shugaban kasar ya ki karbar gudumuwar da Ali Modu Sheriff ya ba shi.
A cewar Hanga, tsohon gwamnan na jihar Borno, ya kawo wannan gudumuwa ana daf da shirya zaben shugaban kasa da aka yi a 2007, lokacin suna ANPP.
KU KARANTA: Sanata Hanga ya ce an yi yarjejeniya za a ba Tinubu mulki a 2023
Ali Modu Sherrif ne kadai ya yi hobbasa
2023: Yan majalisun Arewa sun bayyana yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa, sun ambaci zabinsu
Jaridar ta rahoto Rufai Hanga ya na cewa Ali Modu Sherrif ne kadai gwamnan da ya bada gudumuwa wajen taimaka wa yakin neman zaben Buhari a 2007.
Sanata Ali Modu Sherrif wanda ya yi gwamna tsakanin 2003 da 2011, surukin Muhammadu Buhari ne, amma a karshe bai yi amfani da gudumuwar ta sa ba.
“A lokacin da ya fito takara ta biyu, gwamnoni sun yi taurin-kai. Babu wanda yake shirin bada gudumuwa. Gwamnan da ya yi yunkuri kurum shi ne Modu Sheriff, lokacin ya na mulki a jihar Borno.”
“Shi ne ya bada gudumuwar Naira miliyan 10, ana ranar jajibirin zaben 2007.”
KU KARANTA: Da wuya a kyale mulkin Najeriya ya fada hannun Bola Tinubu - Hanga
“Amma Naira miliyan goma ba su kai ga Buhari ba. Naira miliyan tara aka kawo masa a ranar Juma’a da yamma, kuma za ayi zabe da safe.”
“Wasu suka ce ka da mu yi amfani da kudin domin ta ina za ka kashe Naira miliyan tara, ana gobe zabe?
Tsohon Sanatan ya ce abin da bai sani ba shi ne ko an maida wa Sanata Modu Sheriff, ko kuma sun makale a hanya, a na su bangaren, ba su iya amfani da kudin ba.
Muhammadu Buhari da zaben 2007
Jam’iyyar adawa ta All Nigeria Peoples Party (ANPP) ta zo na biyu a wannan zabe da ya kare a kotu.
Zaben 2007 shi ne na biyu da Mai girma Muhammadu Buhari ya nemi takarar shugaban kasa. Buhari ya sha kashi ne a hannun Alhaji Umaru Musa Yar’Adua.
Asali: Legit.ng