‘Yan Yahoo suna amfani da mata tsirara domin su tafi da imanin jami’anmu inji EFCC

‘Yan Yahoo suna amfani da mata tsirara domin su tafi da imanin jami’anmu inji EFCC

  • Hukumar EFCC ta bankado sabon salon da ‘Yan Yahoo su ka zo masu da shi
  • ‘Yan Yahoo su na ajiye mata su yi tunbur domin a hana jami’an EFCC iya aiki
  • Wilson Uwujaren yace dalilin hakan shi ne rusa hujjojin da hukumar ke nema

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, ta bayyana dabarar da marasa gaskiya su ke yi domin su tsere wa shari’a.

Daily Trust ta rahoto EFCC ta na cewa masu damfarar jama’a ta yanar gizo da “Yahoo boys” suna yi masu amfani da mata tsirara domin kauda masu hankali.

EFCC ta kai hari a otel, ta kama 'Yan damfara rututu

Mai magana da yawun bakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana wannan yayin da yake martani a kan kemen da suka yi a wani otel a Legas.

KU KARANTA: An damke mai taimaka wa IPOB da kwayoyi

Kara karanta wannan

A karon farko Nnamdi Kanu ya fadi yadda aka azabtar da shi, da ya shiga hannu a kasar waje

A ranar Talata, 13 ga watan Yuli, 2021, jami’an EFCC su ka kai samame a wani babban otel mai suna Parktonian a Lekki, su ka yi nasarar cafke mutane 30.

Wadannan mutane watau “Yahoo boys” ko kuma “'Yan Yahoo Yahoo” su na ajiye ‘yan mata su yi tsirara da nufin a hana ma’aikatan EFCC yin aikin da ya dace.

“Jami’an EFCC sun yi amfani da bayanan da suka samu, suka kai wa wasu da ake zargin ‘yan damfara ne mamaya. A harin an cafke mutane 30 da ake zargi da laifi.”
“Daga cikinsu, an tabbatar cewa mutane 24 suna damfarar mutane ta yanar gizo. An kai harin ba tare da an taba kowa ba domin mun dauki makonni mu na sa masu ido.”

KU KARANTA: 'Yan ta'addan IPOB sun hallaka Sojojin Najeriya

‘Yan Yahoo suna amfani da mata tsirara domin su tafi da imanin jami’anmu inji EFCC
Wilson Uwujaren Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC
“Mun iya ware dakunan da aka ajiye wadanda mu ke zargi da wannan laifi.”
“Hukumar ta fahimci akwai wata mummunar dabi’a da ‘yan damfarar su ka bijiro da ita, suna amfani da ‘yan mata da su ke aiki da tsiraicinsu domin a gusar da hankalin jami’anmu, da nufin su iya salwantar da muhimman hujjoji.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: EFCC Ta Kaddamar da Manhajar Tona Asirin Masu Cin Hanci da Rashawa a Najeriya

Jami’an EFCC sun shiga dakunan ba tare da wata matsala ba, kuma ba a muzguna wa sauran mutanen da ke kwance a otel din da ba su ji ba, ba su gani ba,

A safiyar Laraba ku ka ji yadda hadarin mota ya kashe sabon aure a hanyar Abuja. Angon ya mutu nan take, yayin da aka wuce da amaryar zuwa asibiti a Kaduna.

Bayan awa 48 da daura masu aure a garin Kano, mata da mijin suka gamu da hadarin mota. Tuni aka birne mijin a unguwar Shagari Quaters a cikin birnin Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel