A karon farko Nnamdi Kanu ya fadi yadda aka rika azabtar da shi, da ya shiga hannu a kasar waje

A karon farko Nnamdi Kanu ya fadi yadda aka rika azabtar da shi, da ya shiga hannu a kasar waje

  • Lauya ya bayyana wahalar da Nnamdi Kanu ya sha a hannun hukumomi
  • Nnmadi Kanu ya samu damar yin maganan farko tun dawowarsa Najeriya
  • Jami’an DSS suna wurin a yayin da Kanu yake ta ba Aloy Ejimakor labari

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB mai goyon bayan Biyafara, ya bada labarin abin da ya faru da shi da ya shiga hannun jami’an tsaro a kasar Kenya.

Jaridar Premium Times ta ce wannan ne karon farko da Nnamdi Kanu ya yi magana bayan tsare shi.

Lauyan da yake kare jagoran na IPOB, Aloy Ejimakor ya samu damar gana wa da shi a inda yake tsare a hannun DSS, har suka yi sa’o’i uku suna magana.

KU KARANTA: Hanyar da muka bi aka taso keyar Nnamdi Kanu - Minista

The Cable ta ce Ejimakor ya bada labarin abin da Kanu ya fada masa, ya ce Kanu ya fada masa an sanar da wanda suka kama sa ya na tare da ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

“An fada wa mutanen da su kayi ram da shi cewa Kanu mutumin Najeriya ne da yake da alaka da ‘yan ta’adda a kasar Kenya, watakila Al-Shabab.”
“Bayan kwanaki da yawa, sai suka gano gaskiya wanene shi, suka rage muzguna masa. Duk da haka, sun fada masa dole su mika shi ga wadanda su ka aiko su.”

Mista Kanu ya ce babu mamaki jami'an Najeriya ta yi hayar wasu mugaye ne ba tare da sanin gwamnatin Kenya ba, domin su dawo da shi gida, ayi masa shari’a.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Gbajabiamila ya gabatar da rahoton ga Shugaban kasa

Nnamdi Kanu
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban na kungiyar IPOB ya ce an tsare shi na kwanaki babu magana, aka daure shi da sarka a wani mummunan dakin da babu wanda ya san da shi a Kenya.

Bayan haka Nnamdi Kanu ya ce mutanen ba su nuna masa takardar da ta bada dama a cafke shi ba.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya fadawa ‘Yan Majalisa yayin da ya shirya masu liyafa ta musamman a Aso Villa

“Hakika an galabaitar da Kanu, an yi matukar wahalar da shi kamar ba ‘Dan Adam ba a Kenya.”
“Aka rufe masa fuska, aka shiga da shi jirgi ba tare da jami’ai sun duba shi ba. Jirginsu ya bar Nairobi da karfe 12:00 na rana, su ka iso a Abuja da yamma.”

Kwanaki gwamnatin Muhammadu Buhari ta ja-kunne cewa kashin duk wani mai taimakawa tafiyar Mazi Nnamdi Kanu da tallafin kudi da makamai zai bushe.

Ana gudanar da wani bincike na musamman domin a gano inda shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, Nnamdi Kanu, yake samun taimako da goyon-baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel