APC za ta fuskanci wata rigimar cikin gida kan yadda za a shirya zabuka a Jihohi 36

APC za ta fuskanci wata rigimar cikin gida kan yadda za a shirya zabuka a Jihohi 36

  • Jam’iyyar APC ta na sa ran gudanar da zabukan Shugabanni a fadin kasa
  • Matsalar da ake fama da ita, shugabannin APC ba su da cikakkiyar rajista
  • Akwai sabani kan yunkurin bada wasu kujeru ba tare da an shiga zabe ba

Babban rikici ya na jiran jam’iyyar APC mai mulki a game da yadda za a gudanar da zaben mazabu, kananan hukumomi, jiha, har zuwa na kasa.

Ana sauraron yadda za a gudanar da zabukan ba tare da akwai cikakkiyar rajistar ‘yan jam’iyya ba.

Punch ta bayyana cewa baya ga rigimar zabe, akwai rashin jitu wa a game da shirin da manyan jam’iyya suke yi na fito da wasu ‘yan takara.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a mazabar Gwaram

Akwai matsala a rajistar da jam'iyyar APC ta ke da shi

A jihohi 19 ne kadai ake da cikakken rajistar ‘ya ‘yan jam’iyya, an taba rajistar duk sauran jihohin.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Buhari yayi magana kan raba tikitin APC gabannin 2023

Shugabannin jam’iyyar suna kokarin kawo ‘yan takarar da ake so kowa ya mara wa baya ba tare da an yi zabe ba, amma wasu sun ki yarda da wannan.

Jaridar ta ke cewa ana so ne a zakulo wadanda za su rike mukaman jam’iyyar ta APC mai mulki a mazabu, kananan hukumomi da kuma matakan jihohi.

Wani daga cikin kusoshin jam’iyyar, ya shaida wa jaridar cewa su na cikin wani irin mawuyacin hali, ya ce ba su da gamsashen alkaluman ‘yan jam’iyya.

APC NEC
Manyan APC a taro Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ayyukan da Ganduje ya ke yi, ya nuna shi ba mugu ba ne - Buhari

“Abin da mu ke da shi a hedikwata, tsurar sunayen ‘yan jam’iyya ne wanda mu ke tunanin cewa an yi ha’inci a rajistar."
Muna da adadin ‘yan jam’iyya, amma sunaye da hotunansu, ya na hannun jihohi. Dole a tattara su, mu iya hada rajista.”
“Ya za a ce Kano ta na da ‘yan APC miliyan hudu, sai kuma mutum miliyan biyu a Legas? Menene adadin mutanen jihar?

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa sun jero hanyoyi 19 da Buhari zai bi ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali

“Mutum nawa suka yi rajista a zaben da ya wuce? Ka da mu yaudari kanmu. Akwai matsala!”

Jam’iyyar APC za ta gamu da matsala wajen zabukan muddin ba a tantance rajistocin da ke dauke da cikakken bayanin ‘ya ‘yan jam’iyya da aka yi wa rajista ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel