Zaben maye gurbi: APC ta lallasa PDP a mazabar Gwaram ta tarayya dake Jigawa
- Alhaji Yusuf Galami na jam'iyyar APC a zaben maye gurbi na mazabar Gwaram ta tarayya ya lallasa Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP
- Galambi ya samu kuri'u 29,372 daga akwatuna 248 na mazabar inda Inuwa na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 10,047 kuma ya sha kasa
- An yi zaben maye gurbin a ranar Asabar da ta gabata bayan rasuwar dan majalisar wakilai Kila a watan Maris sakamakon rashin lafiya da yayi
Alhaji Yusuf Galami, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da aka yi domin cike kujerar majalisar tarayya ta mazabar Gwaram a jihar Jigawa ya samu nasara.
Farfesa Ahmad Shehu, baturen zaben, bayan tattara kuri'u daga akwatuna 248 ya bayyana Galambi a matsayin mai rinjaye da kuri'a 29,372 a kan Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 10,047.
"Bayan Galambi ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben maye gurbin, ya zama mai nasarar a zaben," Shehu ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Gwaram kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
KU KARANTA: Wanda zai gaje ni sai yayi rusau da ragargazar gidaje fiye da ni, El-Rufai
KU KARANTA: Hotunan daliban Kebbi da jami'an tsaro suka ceto daga wurin 'yan bindiga kwance a asibiti
Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya bayyana bukatar maye gurbin kujerar mazabar Gwaram ta tarayya tun bayan mutuwar Honarabul Hassan Yuguda Kila wanda a da shi ke wakiltar mazabar.
Kila ya rasu ne a asibitin kasa dake Abuja bayan gajeriyar rashin lafiyar da yayi fama da ita a watan Maris, Daily Trust ta ruwaito.
A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji, ta tare motoci manya 12 dankare da shanu 154 tare da kame miyagu 44 a jihar Zamfara, Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Mataimakin kwamandan rundunar, Air Commander Abubakar Abdulkadir, ya sanar da hakan a Gusau a ranar Juma'a yayin mika shanun satan ga gwamnatin jihar Zamfara.
Abdulkadir ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke tafe da shanu 154, rakumi daya da kuma rago daya a manyan motoci kan hanyarsu ta zuwa Gusau.
Asali: Legit.ng