‘Yan Majalisa sun jero hanyoyi 19 da Buhari zai bi ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali
Majalisar wakilan tarayya ta gabatar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu shawarwari a kan yadda matsalar tsaro zai zama tarihi a Najeriya.
Jaridar The Cable ta ce duk ‘yan majalisa sun amince da wannan rahoto da aka mika wa shugaban kasa.
Kwamitin da aka kafa ya kammala aikin da aka ba shi
A watan Afrilu ne aka kafa wani kwamiti na musamman da zai shirya taro kan batun tsaro domin ya fito da dabarun da za a bi wajen kawo zaman lafiya.
Bayan wannan kwamitin ya kammala aikinsa, shi ne shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya kai wa Muhammadu Buhari rahoton da aka yi.
1. A ba jami’an ‘yan sanda 40, 000 masu kwantar da tarzoma horas wa na musamman. Sai a tura ‘yan sandan zuwa kowane bangare a kasar nan.
2. A kirkiro wata tawaga a cikin dakarun ‘yan sanda da za su tsare dajojin Najeriya. Wadannan jami’ai su zauna a karkashin sa idon jihohi 36.
3. Ofishin NSA da na CDS su bankado duk wasu bata-gari da ke cikin jami’an tsaro.
KU KARANTA: Dole mu yi abin da za mu iya, mu kawo zaman lafiya – Buhari ga ‘Yan Majalisa
4. Fadar shugaban kasa ta dauko shirin gyara tsare-tsare da aikin ‘dan sanda a Najeriya.
5. A fitar da kudi domin a saya wa jami’an tsaro kayan aikin da su ke matukar bukata.
6. Ayi aiki da kamfanonin tsaro na kasuwa da za su taya gwamnati yaki da ‘yan ta’adda.
7. Masu iko su wajabta wa duk wasu jami’an tsaro yada wa junansu bayanan da ake bukata.
8. A kafa na’urorin CCTV a tituna da hanyoyi da wuraren shakata wa a manyan birane.
9. A kirkiro cibiyar da za a kira NCC da za a iya tuntuba domin magance matsalolin tsaro.
10. A karfafa wa NOA da ma’aikatar yada labarai su shiga wayar da mutane a kan hadin-kai.
KU KARANTA: Hukumar NFIU ta kori Ma’aikatan da ke neman taba Atiku da Tinubu
11. A kafa kwamitocin tsaro a kananan hukumomi da zai kunsho shugabannin gargajiya.
12. A ware wurare na musamman domin kiwon dabbobi a wuraren da ake da karancin mutane.
13. A karfafa aikin bangaren shari’a, ta haka za a rika hukunta wadanda aka samu da laifi.
14. A samar da rajistar da za a rika ajiye sunayen masu laifi da duk bayanansu.
15. A rage dogara da kamfanonin kasashen ketare wajen sayen kayan makamai.
16. Ya zama dole gwamnatin tarayya ta yi maganin talaucin da ake fama da shi.
17. Jami’an tsaro su yi bincike su gano shugabannin masu tada kafar baya a Najeriya.
18. Hukumomi su takaita shigowar makamai, a kuma rika karbe makaman da aka samu.
19. A hukunta duk wanda aka samu ya na dauke da makami ba tare da izini ba.
Asali: Legit.ng