Shugaban kasa Buhari ya yabi Ganduje, ya ce Gwamnan Kano ba mugu ba ne

Shugaban kasa Buhari ya yabi Ganduje, ya ce Gwamnan Kano ba mugu ba ne

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu yabo daga shugaba Muhammadu Buhari
  • Shugaban kasar ya ji dadin yadda Gwamnan Kano ya ke karasa ayyukan baya
  • Abdullahi Ganduje ya kammala kwangilolin da gwamnonin baya ne suka bada

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabi gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yayin da ya ziyaci jihar Kano a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuli, 2021.

Mai girma Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnan na Kano ba mugun shugaba ba ne.

Shugaban Najeriyan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wa Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a fadar sa bayan kaddamar da aikin jirgi.

KU KARANTA: Sanusi II ya yabi Malaman Kano a kan tunkarar Sheikh Kabara

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kasar ya yabi Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kan irin ayyukan cigaba da more rayuwan da gwamnatinsa ta yi a Kano.

Muhammadu Buhari ya ce karasa ayyukan gwamnonin baya da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ke yi, ya nuna cewa shi shugaba ne na kwarai.

Kara karanta wannan

Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

Shugaban kasar ya ce ya ji dadin ganin yadda gwamnan na Kano ya kirkiro wasu ayyukan a gwamnatinsa, kuma ya karasa su domin jin dadin al’umma.

Amma duk da haka bai manta da ayyukan da ba shi ya kirkiro su ba, hakan ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya yabi gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Shugaban kasa Buhari da Ganduje
Shugaba Buhari a Kano Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: El-Rufai zai yi wa Malamai jarrabawa a Kaduna

“Hakan ya nuna shi ba mugu ba ne ko maketaci.”

The Cable ta rahoto Shugaba Buhari ya na cewa da yi wa mutane abubuwan more rayuwa ne kurum Ganduje zai gaskata cewa jihar Kano ta na samun kudi.

“Ta yin hakan ne kurum za a iya gani, a shaida dukiyar da ake samu a madadin jihar Kano.”

Shugaba Buhari ya yi mutane a Kano

A jiyan kun ji cewa an ga cincirindon jama’a yayin da Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin gina jirgin kasan Kaduna-Kano mai tsawon kilomita 203.

Kara karanta wannan

Ka inganta tsaro, rangwantawa talakawa da rage farashin kaya, Sarkin Kano ga Buhari

A na sa bangaren, Abdullahi Umar Ganduje ya gode wa Muhammadu Buhari da ya ba mutanen jihar Kano mukamai masu tsoka, tare da yi wa jihar ayyuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng