Dagacin kauye ya kai kuka game da harin da Dorina ke kaiwa kaiwa mutane a Gombe
- Dorinar ruwa ta lalata gonakin shinkafa da dama a wani kauyen Gombe
- Manoma sun kirga dimbin hasarar da ta haddasa musu
- Wadansu manoman da suke samun buhu 100 yanzu sun koma samun 70
Adamu Sambo, mai rike da sarautar gargajiya a ƙauyen Kupto da ke Karamar Hukumar Funakaye ta Jihar Gombe, ya nuna damuwarsa kan barnar da wata dorinar ruwa take yi a gonakin yankin.
Malam Sambo, Magajin Garin Kupto, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Kupto, a ranar Alhamis, ya ce dabbar ta kasance tana addabar mutane da lalata amfanin gona a filayen noma.
A cewarsa, dorinar ruwan takan fito ne da daddare, ko kuma da sanyin safiya lokacin da ko ina ya yi tsit domin yin “barna a gonaki da lalata amfanin gona.’ ’
Ya ce lamarin ya sanya manoma komawa ga kwana a gonakinsu domin kare amfaninsu tare da hana dabbar lalata gonakin.
Yace:
“Galibi miyagun dabbobin suna fitowa cikin a daruruwansu, inda suke lalata kusan kowane irin amfanin gona da aka noma.
"Ba ma son mu dauki doka a hannunmu saboda an sanar da mu cewa dorinar ruwa na daga cikin halittu masu hadari kuma doka ta kiyaye su."
KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane
KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD
Ya kara da cewa manoman rani a yankin tuni suka fara shaida asarar da suka yi saboda hare-haren miyagun dabbobin sun haifar da karancin amfanin gona da kuma karancin kudin shiga a gare su.
"Manoman rani da ke girbar buhun shinkafa 100 sun tashi da buhu 30 kuma wadanda ke girbar buhu 30 sun tashi da buhu 10-15, '' inji shi.
Malam Sambo ya ce duk da cewa al'ummar ba su gabatar da rahoto a hukumance ga hukumomin da abin ya shafa ba, amma, "yanzu haka muna kira ga gwamnati da ta kawo mana dauki."
NAN ta ruwaito cewa mafi yawan manoma daga sauran kauyukan da ke kewaye, musamman manoman shinkafa, sun fuskanci irin wannan barnar.
Da yake maida martani game da batun, Inuwa Ahmed, Daraktan kula da gandun daji da namun daji na Jihar Gombe na Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Daji, ya ce ma’aikatar na sane da harin dorinar ruwan da take kai wa a gonakin kauyen Kupto.
Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane
A bangare guda, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed AbdulKadir ya bayyana cewa ya san wadanda ke daukan nauyin masu tada zaune tsaye a jiharsa.
Gwamnan wanda yayi wannan furuci yayin rabawa mutane kudin jari a karamar hukumar Darazo na jihar ranar Talata ya lashi takobin tona asirin masu daukar nauyin hare-hare a lokacin da ya dace, rahoton DailyTrust.
Ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa yan siyasa ke kawo yan ta'adda jihar.
Asali: Legit.ng