Khalifa Sanusi II ya jinjinawa Malaman da suka kalubalanci Abduljabbar, ya yi kira ga al'umma

Khalifa Sanusi II ya jinjinawa Malaman da suka kalubalanci Abduljabbar, ya yi kira ga al'umma

  • Muhammadu Sanusi II ya yabi zaman da aka yi Abduljabbar Kabara a Kano
  • Tsohon Sarkin ya ji dadin abin da ya faru, yace gaskiya ta fito a wannan zama
  • Khalifan na Darikar Tijjaniya yace Allah ya azurta Kano da manyan Malamai

Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan mukabalar da aka yi a Kano, inda ya yabi malaman, ya kuma yi kira ga hukuma ta yi abin da ya dace.

“Godiya ce za mu yi ga malamai na Kano na tsaya wa wajen kare janibin Manzon Allah tsira ga amincin Allah su tabbata a gare sa.”
“A wajen muqabala da aka yi jiya (ranar Asabar), mun ga su Malam Rabiu Umar Rijiyar-Lemu, Malam Abubakar Madatai, Malam Kabir Bashir da Malam Mas’ud Mas’ud Hotoro, mun gode masu a kan abin da suka yi; na nuna ilmi, da abin da su ka tabbatar a kan wadannan maganganu da an dade ana jinsu.”

Kara karanta wannan

A karon farko Nnamdi Kanu ya fadi yadda aka azabtar da shi, da ya shiga hannu a kasar waje

KU KARANTA: Tambayoyin da Malamai su ka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara

“Kuma mutanen Kano sun gode wa wadannan malamai wadanda almajiran manyan malamai ne, shehunnansu duk mutanen Kano ne, wannan ya nuna arzikin da Allah ya yi wa kasar mu na malamai.”
“Malamai sun gama na su, yanzu ya rage ga hukumomi su san abin da za su yi. Amma an sauke hakki, Duniya ta gani”

Khalifa Sanusi ya cigaba da addu'a:

"Allah ya tsare gaba. Mu na kira ga jama’a su dage a kan kare Manzon Allah SAW da iyalanSa, da Ahlul Baiti, da SahabbanSa."
"Malamai su cigaba da sauke wannan nauyi da suka dauka. A zauna lafiya, a bar hukumomi su dauki matakin da ya dace."

KU KARANTA: Sheikh Yabo ya yabawa Abduljabbar Kabara hukuncin kisa

Khalifa Sanusi II ya jinjinawa Malaman da suka kalubalanci Abduljabbar, ya yi kira ga al'umma
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi II Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

A karshe tsohon Sarkin ya yi kira ga mutane su yi abin da ya kamata, ya roki Ubangiji Madaukakin Sarki ya kare daraja da kimar addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

Wani Bawan Allah mai suna Ibrahim El-Caleel ya wallafa wannan bidiyo a shafinsa na Facebook, ya na cewa: “Khalifa Malam Muhammadu Sanusi II (Hafizahullah) dama ya daɗe yana yaƙar mugayen aƙidu masu sakin harshe akan haƙƙoƙin Manzon Allah ﷺ da kuma Sahabban Sa.”

Ya kuma ce: “Allah Ya ƙara mishi albarka, da shiriya, da imani, da gam-da-ƙatar. Allah Ya ƙara mana ƙaunar Manzon Allah."

Basaraken dama kullun idan aka samu yanayi irin wannan, baya ƙasa da gwiwa wajen fitowa yayi nasiha, ya yi Allah wadai da masu yaɗa ɓarnar.

Dazu kun ji cewa larura ce ta jawo Farfesa Salisu Shehu ya yarda ya zama Alkalin muqabalar da aka yi.

Farfesan ya ce saura kiris ya ki karbar tayin zama Alkali a zaman sauran malaman Ahlus-Sunnah da Abduljabbar Nasiru Kabara, amma haka Allah ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng