A kara farashin litan man fetur zuwa akalla N380, Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifaki

A kara farashin litan man fetur zuwa akalla N380, Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifaki

- Kungiyar gwamnonin Najeriya NGF ta yi zama ranar Laraba a Abuja

- Da alamun yan Najeriya zasu fuskanci sabon farashin man fetur

- Gwamnonin sun bada shawaran cire tallafin mai gaba daya

A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba lamarin cire tallafin man fetur.

Za ku tuna cewa shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya bayyana a kowani wata ana kashe N120bn don biyan kudin tallafi.

Punch ta rahoto cewa a yayin zaman gwamnonin da ya gudana ranar Laraba, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda shine shugaban kwamitin ya gabatar da rahoton bayan tattaunawa da sukayi.

Yayi bayanin cewa ba zai yiwu a cigaba da biyan kudin tallafin mai ba saboda masu fashin kwabri da manyan yan kasuwa kawai ke amfana.

Kwamitin ta bada shawaran cewa a cire tallafin mai domin ceton tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Wannan abin takaici ne - PDP ta yi martani cikin fushi kan ficewar gwamna Ayade zuwa APC

A kara farashin litan man fetur zuwa akalla N380, Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifaki
A kara farashin litan man fetur zuwa akalla N380, Gwamnonin Najeriya 36 sun yi ittifaki
Asali: Twitter

DUBA NAN: Shugabannin PDP sun shiga ganawa kan sauya shekar gwamnan Kross Ribas

El-Rufa'i yace, "Ana kashe tsakanin N70bn da N210bn kowani wata don kawai a cigaba da sayar da litan mai a N162, wannan ko uwar kudi bai kai ba kuma kudin dake shigowa gwamnati zai ragu da N50bn a kowani wata."

"Ta wani dalili zamu cigaba da sayar da mai a N162? "

Ya kara da cewa jihohi 12 kadai ke shan kashi biyu cikin uku na man feturin Najeriya,

A karshe, kwamitin ta bada shawaran cewa a fara sayar da mai a farashin N408.5 ga Lita amma idan kungiyoyin kwadago suka matsa, a sauko da shi N380.

A riwayar Thisday, gwamnonin sun ce a fara sayar da man akalla N385/l.

A wani labarin kuwa, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ranar Alhamis, ya ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi guda uku da gwamnatinsa ta siyo wa rundunar sojin sama (NAF), kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Shugaban ya miƙa jiragen ne a sansanin sojin dake Makurɗi yayin bikin cikar NAF shekaru 57 da kafuwa.

Shugaba Buhari, wanda ministan tsaro, Bashir Magashi, ya wakilta yace jiragen yaƙin JF-17 da aka ƙara zuwa kayan aikin NAF zasu taimaka sosai wajen yaƙin da rundunar take yi da yan ta'adda, yan bindiga da sauran manyan laifuka da ƙasar ke fama dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel