Za a gamu da gagarumin yajin-aiki idan aka biyewa Gwamnoni, aka kara kudin fetur inji NLC

Za a gamu da gagarumin yajin-aiki idan aka biyewa Gwamnoni, aka kara kudin fetur inji NLC

- Kungiyar NLC ta yi wani zama a kan batun kudin man fetur a Najeriya

- ‘Yan kwadago ba su goyon bayan a maida farashin litar man fetur N380

- Gwamnoni sun bada shawarar a koma saida mai daga N380 zuwa N408

Kungiyar kwadago ta kasa ba ta yi na’am da shawarar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bada na tsaida farashin fetur a tsakanin N380 da N408 ba.

Jaridar Punch ta ce akwai neman takalo rigima da rashin tausayin al’umma a matsayar da kungiyar NGF ta dauka na cewa a daina biyan tallafin mai.

Idan aka yi la’akari da halin da ‘yan Najeriya ke ciki, musamman ma’aikata, kungiyar kwadago ta ce bai dace a bada shawarar a kara farashin litar mai ba.

KU KARANTA: Kwamitin Gwamna El-Rufai ya na so litar fetur ya kai N408

NLC ta ce: Ko da karin 1% aka yi a kan abin da ake saida kayan mai, musamman fetur, hakan zai jawo mu janye hannunmu, ma’aikata a fadin kasar nan su tafi yajin-aiki ba tare da an sanar da lokacin dawo ba.”

A wata takarda da majalisar koli ta NEC ta fitar bayan zaman da ta yi a ranar Talata a Abuja, kungiyar ta yanke shawarar ta kai wa gwamnati kukanta.

Kungiyar NLC ta rubuta takarda zuwa ga gwamnatin tarayya, ta sanar da ita game da harin da ma’aikata suke ciki, da matakin da suka dauka a kan batun.

Shugaban NLC na kasa, Ayuba Wabba, da sakatarensa, Ismail Bello sun sa hannu matsayar da aka dauka, suka tabbatar da rashin goyon bayan karin kudin mai.

KU KARANTA: Ministan shari’a ya sa aka samu cikas wajen karbo $60bn daga Amurka

Za a gamu da gagarumin yajin-aiki idan aka biyewa Gwamnoni, aka kara kudin fetur inji NLC
Kungiyar NLC Hoto: www.nairametrics.com
Asali: UGC

Har ila yau, NLC ta ce ba ta cikin wata yarjejeniya da gwamnati kan maganar tsaida farashin mai ba, ta ce zaman da aka shirya za ayi a kwanaki bai yiwu ba.

Takardar ta ce: “NEC za ta tuna an dakatar da zaman da aka shirya za ayi a Fubrairu, tun lokacin kuma ba a sake wani zama ba, gwamnati ba ta kira taro ba.”

Jaridar The Nation ta ce NLC ta sanar da sauran takwororinta su fara shirya wa tafiya yajin-aiki, idan gwamnati ta karbi shawarar NGF, ta kara farashin fetur.

A kwanakin baya, kungiyar gwamnonin Najeriya NGF karkashin Gwamna Kayode Fayemi, ta kafa kwamiti na musamman domin duba batun cire tallafin mai.

Za ku tuna cewa shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce tallafin yana cin N120bn a wata. Hakan ya sa NGF ta bada shawarar janye tallafi, sai a kara farashin lita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel