Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD da kuma saka matarsa tana karbar albashi daga cocin
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta maka wani fasto mai suna Omosebi Fred Adeola a gaban kotun Abuja
- Adeola ya fada komar hukumar ne bisa zargin karkatar da kudin coci don amfanin kansa da cin zarafin mutane, da sauran zarge-zarge
- Faston an kuma ce ya shigar da sunan matarsa a jerin masu karbar albashi daga cocin wanda hakan cin amanar matsayinsa na shugaban cocin ne
Wani mai ikirarin Fasto ne shi mai suna Omosebi Fred, ya gurfana a gaban kotu kan zargin karkatar da kudin cocin har na naira miliyan 15 da rabi.
An gurfanar da Adeola a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja da Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) kan tuhume-tuhume 11 kan zargin karkatar da kudin cocin.
Zarge-zargen, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa, sun hada da zargin "hada baki da cin amanar mukamin ofis da karkatar da kudade."
'Yan Najeriya sun yi tsokaci kan batun cewa faston da ya yi amfani da kudaden taimako na cocin don amfanin kansa ciki har da biyan kudin digirinsa na uku a Jami'ar Babcock (BU).
Faston, wanda kuma babban Darakta ne a wata kungiyar agaji, an ce ya shigar da matarsa ba bisa ka’ida ba a cikin albashin cocin.
Yana dai fuskantar shari’a ne a gaban Mai shari'a A.O Otaluka na kotun da ke Apo, Babban Birnin Tarayya Abuja.
KU KARANTA: Shugaba Buhari na yiwa gwamnoninmu barazana, Jam'iyyar PDP
DUBA NAN: Gwamnatin Buhari ba ta iya magance rashin tsaro ba - Kukah ya fada wa Amurka
'Yan Najeriya sun maida martani
A halin da ake ciki, ‘yan Najeriya a shafukan sada zumunta na mayar da martani game da kamun faston bayan wani bayani da hukumar EFCC ta fitar a ranar Talata, 13 ga watan Yuli.
Wani mai suna Dupssybabby ya rubuta:
"Shin kudaden Coci sun shafi EFCC ne? Membobin Cocin ba za su iya barin hukunci a hannun Allah ba. Allah ya taimake mu."
Wani mai suna Pyramid Properties ya yi tsokaci:
"A karshe, an kama shi. Godiya ta tabbata ga Allah. Da fatan kuma da yardar Allah, za a gabatar da abokan aikinsa su ma. A kula, Mr Omosebi Adeola ba fasto ba ne amma memba ne na cocin."
Wani kuma mai suna Covidquin ya yi sharhi da cewa:
"Wannan shi ne dalilin da ya sa na daina zuwa coci. Kashi 90% na fastoci barayi ne."
Asali: Legit.ng