Jerin manyan jihohin Najeriya 10 da ke da sauƙin yin kasuwanci

Jerin manyan jihohin Najeriya 10 da ke da sauƙin yin kasuwanci

Wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar ya nuna cewa majalisar ba da izinin kula da harkokin kasuwanci ta shugaban kasa (PEBEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta wallafa bincike kan wuraren da ke da saukin yin kasuwanci na kasa.

Kowace jiha an auna ta a ma'auni mai maki 10 a duk bangarori hudu kamar su kayayyakin more rayuwa da tsaro, nuna gaskiya da samun bayanai, muhalli mai tsari da kuma karfin ma'aikata.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Bidiyon Shagari yana kunna sigari lokacin da Firayim Minista Tafawa Balewa ke jawabi ga taron jama'a

Jerin manyan jihohin Najeriya 10 da ke da sauƙin yin kasuwanci
An wallafa rahoton majalisar ba da izinin kula da harkokin kasuwanci ta shugaban kasa (PEBEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo Hoto: @professoryemiosinbajo
Asali: Facebook

Waɗannan manuniya sun ba da tushe wajen ƙididdigar ayyukan jihar gaba ɗaya. An gudanar da binciken rahoton da KPMG Professional Services ya gina tsakanin Nuwamba 2020 da Janairu 2021.

Gombe da maki 7.69 ta ci gaba da kasancewa kan gaba a wurare mafi saukin yin kasuwanci a kasar fiye da sauran jihohi da Babban Birnin Tarayya (FCT).

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Ga jerin manyan jihohi goma da ke kan gaba a cikin jihohi 36 na kasar

1. Gombe

2. Sokoto

3. Jigawa

4. Bauchi

5. Akwa Ibom

6. Kebbi

7. Anambra

8. Ondo

9. Katsina

10. Bayelsa

Manufofin Gwamnatin Buhari sun ba mutum miliyan biyu abin yi cikin shekara 1 inji Osinbajo

A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta sama wa mutane har fiye da miliyan biyu hanyar cin abinci a Najeriya.

Mai girma Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa mutane da-dama sun samu aiki ne ta sanadiyyar tsarin tattalin arzikin da su ka shigo da shi.

Jaridar The Cable ta ce Yemi Osinbajo ya yi wannan ikirari a lokacin da aka yi wani taro da kwamitin ESP ta yanar gizo a ranar 5 ga watan Yuli, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel