Gwamnatin Tarayya ta ba Dangote kwangilar yin hanyoyi a maimakon ya biya haraji

Gwamnatin Tarayya ta ba Dangote kwangilar yin hanyoyi a maimakon ya biya haraji

  • Majalisar FEC ta amince da kwangilolin titunan da aka ba kamfanin Dangote
  • Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ya ce Dangote zai gina hanyoyin N300b
  • Dangote zai gina tituna a Kaduna, Borno, da Legas a maimakon ya biya haraji

Nairametrics ta ce Majalisar zartar wa ta kasa watau FEC ta amince da kwangilolin titunan da aka ba kamfanin Dangote a kan kudi Naira biliyan 309.9.

A zaman da aka yi na ranar 14 ga watan Yuli, 2021, aka amince cewa kamfanin na Dangote zai gina hanyoyin kilomita 274.9 a madadin ya biya haraji.

Yadda abin ya ke - Babatunde Fashola

Vanguard ta ce Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola ya bayyana wa manema labarai haka bayan tashi taron na FEC jiya a Abuja.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya karya dokar yaki da COVID-19

Babatunde Fashola ya ce wannan ne karo na biyu da ma’aikatarsa ta ke ba kamfanin irin wannan kwangila da nufin a dauke masa nauyin biyan haraji.

Kara karanta wannan

Yadda na zama Alkalin mukabalar Abduljabbar Kabara da Malamai inji Salisu Shehu

“Wadannan tituna biyar masu tsawon kilomita 274.9 za su ci N309, 917, 717, 251.35, Dangote zai gina su, sai a yafe harajin da za a karba a hannunsa.”
Hanyoyin sun hada da Bama zuwa Banki a Borno a kan Naira biliyan 51.02 da zai ci 49.15km, Dikwa zuwa Gamboru-Ngala mai tsawon 49.58km da zai ci Naira biliyan 55.5, sai titin Nnamdi Azikiwe a Kaduna mai tsawon 21.48km a kan Naira biliyan 37.56."

Sauran kwangilolin su ne na titin Epe zuwa Shagamu da Obele/Ilaro/Papalanto zuwa Shagamu a jihohin Legas da Ogun, gaba daya za su ci Naira biliyan 165.83.

KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa na shirin tura sunan Onochie a karo na biyu

Gwamnatin Tarayya ta ba Dangote kwangilar yin hanyoyi a maimakon ya biya haraji
Dangote da Mataimakin Shugaban kasa Hoto: metrowatchonline.com
Asali: UGC

Ministan ya ce wannan tsari da aka kawo yana cikin manufofinsu na ganin an fadada yadda ake aiwatar da kwangila, musamman ta yunkurin shigo da ‘yan kasuwa.

Wannan tsari ya na nan dama a kasa

Kara karanta wannan

Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari

Har ila yau, Ministan ya yi karin haske da cewa gwamnatin baya ta kawo irin wannan tsari, amma ba ta yi amfani da shi, sai da gwamnatin nan ta zo, aka duba batun.

A watan Afrilun 2021, hukumar FIRS mai karbar haraji ta ba kamfanin Dangote Industries satifiket, inda aka dauke masa biyan harajin Naira biliyan 22.321.

Jaridar ta ce a madadin haka, wannan kamfanin zai gina titin Apapa-Oworonshoki-Ojota a Legas, da hanyar Lokoja-Obajana-Kabba da ta ratsa jihohin Kogi da Kwara.

Ku na da labari cewa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yabi Gwana Abdullahi Ganduje yayin da ya tashi da kyautar gwamnan da ya fi kowa aiki.

Dr. Abdullahi Ganduje ya samu lambar yabo saboda kokarinsa na gina abubuwan more rayuwa da gyara ilmi, ya ce karatun firamare zuwa sakandare kyauta ne a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel