Hanyar da mu ka bi aka taso keyar Nnamdi Kanu bayan shekaru 2 ana nemansa inji Minista

Hanyar da mu ka bi aka taso keyar Nnamdi Kanu bayan shekaru 2 ana nemansa inji Minista

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda Nnamdi Kanu ya shigo hannun Hukuma
  • Lai Mohammed ya ce an dauki sama da shekaru biyu ana neman Shugaban IPOB
  • Mohammed ya ce wasu kasashen waje sun taimaka wajen cafke wannan mutum

Gwamnatin tarayya ta sake yin karin bayani a kan yadda ta cafko Mazi Nnamdi Kanu mai jagorantar kungiyar IPOB, daga kasar waje zuwa Najeriya.

Jaridar The Nation ta rahoto Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed, ya na bayanin yadda gwamnati ta kama Nnamdi Kanu wannan karo.

Alhaji Lai Mohammed ya ce wasu kasashen ketare da jami’an tsaro masu samun bayanai ne suka taimaka wajen ganin Nnamdi Kanu ya shiga hannun hukuma.

KU KARANTA: Hukuma ta na neman sirrin tafiyar IPOB da aikin rediyon Biyafara

Da yake jawabi a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, 2021, Ministan bai ambaci sunayen kasashen wajen da su ka taimaka wa Najeriya a wajen wannan aikin ba.

Mohammed ya shaida wa manema labari dazu da safe a garin Abuja cewa gwamnatin tarayya ta yi nasarar kama shi ne bayan shekara biyu ana nemansa ido-rufe.

Yadda aka yi - Lai Mohammed

“Ku na da masaniya cewa an kama shugaban kungiyar IPOB da aka haramta aikinta, Mista Nnamdi Kanu, an dawo da shi gida, za a cigaba da shari’a da shi a kotu.”
“Abin da zan iya fada shi ne jami’an tsaronmu masu kokari ne suka hada-kai da kasashen da mu ke da yarjejeniya da su. Za mu cigaba da girmama yarjejeniyarmu.”

KU KARANTA: Kanu zai iya amsa laifin hannu wajen kashe-kashen mutum rututu

Nnamdi Kanu
Mazi Nnamdi Kanu Hoto: Getty Images
Asali: UGC

An dade ana neman Kanu ruwa a jallo

“Abin da zai kayatar da mutanen Najeriya shi ne mun shafe fiye da shekaru biyu, jami’an leken bayanan mu suna neman shugaban na haramtacciyar kungiyar IPOB.”
“Ya na rayuwar jin dadi ne a kasashen ketare, ya na yawo a jiragen sama, ya na zama a katafaran gidaje, ya na cikin tufafi masu tsada, ya na taka takalman kece-raini.”
“Kamar yadda kowa ya gani, an ga ya na sanye da tufafi mai tsada na kamfanin kasar Italiya, Fendi, a lokacin da aka kama shi.”

Ministan ya gode wa hukumomin kasar waje da su ka ba Najeriya hadin-kai wajen cafko Kanu, sannan ya yaba da kokari da kwarewar da jami’an tsaron Najeriya su ka nuna.

Kun ji labari wata kungiya mai kare 'yancin Bil Adama Adam da bin dokoki ta ce da makusantan Nnamdi Kanu aka hada kai da su, aka kama shi a makon da ya wuce.

Kugiyar ta International Society for Civil Liberties and Rule of Law, ta ce na-kusa da Mazi Nnamdi Kanu ne su ka ci amanar shi, har ya fada hannun hukumomin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel