Kashin duk wani Mai taimakawa tafiyar Nnamdi Kanu da tallafin kudi da makamai zai bushe

Kashin duk wani Mai taimakawa tafiyar Nnamdi Kanu da tallafin kudi da makamai zai bushe

  • Masu bincike sun karbe duk wayoyin salulan Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
  • Rahotanni sun ce ana bincike domin tona masu taimaka wa kungiyar IPOB
  • Jami’an tsaro suna son gano wadanda ke ba Kanu goyon bayan kayan aiki

Ana gudanar da wani bincike na musamman domin a gano inda shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra, Nnamdi Kanu, yake samun taimako.

A ranar Laraba, 30 ga watan Yuni, 2021, The Nation ta fahimci cewa jami’an tsaro su na binciken lambobin wayoyin da Nnamdi Kanu yake kira a salula.

Bayan nan, ana bin diddikin kafofin sadarwa da yada labarai da shugaban haramtacciyar kungiyar mai fafatukar kafa kasar Biyafara ya ke bibiya.

KU KARANTA: Shugaban IPOB, Kanu, ya bayyana a gaban Kotu

Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu ya shiga hannu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Makasudin wannan bincike shi ne a iya gano mutanen da su ke taimaka wa tafiyar IPOB da kudi.

Majiyar jaridar ta ce masu binciken Mazi Nnamdi Kanu sun dukufa wajen gano abubuwan da su ke cikin wayarsa domin a lalubo masu daure masa gindi.

“Bayan an cafke Kanu, an karbe wayoyin salularsa, an raba shi da su. Bai iya samu ya yi magana da kowa ba tun daga lokacin.”
“Masu bincike suna neman gano masu mara masa baya a gida da waje, da kuma sojojinsa, da masu tsara danyen aikin da yake yi.”

KU KARANTA: Dillalan makaman Duniya suna tare da Nnamdi Kanu

“Za a toshe duk wasu akawun da ke da alaka da Nnamdi Kanu har zuwa lokacin da za a kammala binciken da aka yi.”
“Abin da masu binciken su ke nema shi ne inda kungiyar IPOB ke samun makamai da yadda ake gudanar da aikin rediyo Biyafara.”

Ana sa ran cewa idan duk an gano wadannan, gwamnatin tarayya za ta yi wa Duniya bayanin yadda aka kafa kungiyar mai rajin barkewa daga Najeriya.

Rahotanni suna yawo cewa wata mace aka yi amfani da ita, aka taso keyar Nnamdi Kanu gida. Wannan mata ta na aiki ne da jami’an tsaron Najeriya a boye.

Nnamdi Kanu ya na da takardar zama ‘dan kasar Ingila kamar yadda yake mutumin Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng